Maciji ya sari magidanci yayin da yake zaune a masai yana latsa wayarsa

Maciji ya sari magidanci yayin da yake zaune a masai yana latsa wayarsa

  • Wani magidanci 'dan kasar Malaysia ya bayyana yadda maciji ya sare sa a mazaunensa yayin da yake kni tukunyar masai yana wasa da wayar hannunsa
  • Yayin hanzarin bude kofar bandakin, sai da ya balle kofar inda ya garzaya asibiti don samun riga kafin gaggawa, amma ga mamakinsa macijin ba mai dafi bane
  • Ya bayyana yadda rabin hakorin macijin ya makale a mazauninsa, ya dauki tsawon makwanni 2 yana amfani da bandakin masallacin kusa da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani maciji da ya dade yana kwantan bauna a bandakin wani mutum ya sare sa a mazaunensa yayin da mutumin ke kan tukunyar masai rike da wayarsa yana wasa da ita.

Sabri Tazali, daga kasar Malaysia ya rayu bayan farmakin da macijin ya kai masa, Shafin LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Anambra: Osinbajo ya yi martani kan kisan 'yar Arewa da 'ya'yanta 4 a jihar Kudu

Maciji ya sari magidanci yayin da yake zaune a masai yana latsa wayarsa
Maciji ya sari magidanci yayin da yake zaune a masai yana latsa wayarsa. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda ya bayyana bayan farmakin da macijin ya kai masa ya yi "sa'a" kasurgumin macijin bai sare sa a al'aurarsa ba.

Yadda macijin ya sari mutumin

Macijin ya sari Tazali, mai shekaru 28 yayin da yake tsaka da amfani da bandaki a gidansa cikin garin Selayang a jihar Selangor dake kasar Malaysia inda yaji wani irin sara mai kaifi a mazaunensa.

Bayan yaji alamar sarar macijin a mazaunensa, Tazali ya yi hanzarin mikewa gami da cafko macijin tare da buga sa da bangon bandakin.

Cikin firgici, daga nan ne ya balle kofar bandakin yayin kokarin budewa cikin hanzari.

Sai dai a sa'ar Tazali, macijin ba mai dafi bane.

Nan take ya garzaya asibitin karamar hukumar don a duba masa ciwon sa tare da samun allurar magani daga likitoci.

Kara karanta wannan

Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari

Daga bisani, 'yan kwana-kwana suka isa gidan don cire macijin.

Tazali ya bayyana wa kananan jaridu yadda har yanzu yake cikin wani yanayi na firgici bayan farmakin da macijin ya kai masa, hakan yasa ya koma amfani da bandakin masallacin kusa da su na tsawon makwanni biyu a maimakon nasa.

Yayin wallafa bidiyon a kafafan sada zumuntar zamani, ya rubuta: "Wani maciji ya sari mazaunai na. Macijin ya fito ne daga cikin tukunyar masai."
Ya kara da cewa: "Cikin sa a, bai ciji kwayayen haihuwana ba."

Ya cigaba da bayyana yadda cikin firgici ya tumbuko "rabin hakorin macijin" daga mazaunansa inda macijin ya saresa. Ya zargi cewa hakorin ya balle ne yayin da ya "bugi macijin da karfi" gami da jefar da shi jikin bango.

A halin yanzu, Tazali ya canza tukunyar masan mai kalar hanta da dalleliyar sabuwar fara yadda zai iya ganin cikin yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel