Tsadar Rayuwa: 'Yan Sanda Sun yi Ram da Iyayen da Suka Saka Ɗansu a Kasuwa

Tsadar Rayuwa: 'Yan Sanda Sun yi Ram da Iyayen da Suka Saka Ɗansu a Kasuwa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta cafke wasu iyaye bisa zargin yunkurin sayar da dansu bayan sun saka shi a kasuwa
  • Iyayen yaron, Uchenna da Chineye Eziwkwe sun ce dole ce ta saka su daukar danyen matakin saboda matsin rayuwa
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya ce an ceto yaron kuma ana kara bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Lagos- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta yi ram da wasu iyayen da su ka sa dansu a kasuwa domin su samu kudin ficewa daga kasar nan. Uchenna Eziekwe mai shekaru 28 da matarsa Chineye Eziekwe mai shekaru 22 sun bayyana aniyarsu ta sayar da dan a asibitin Isolo General Hospital a Legas.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta yi fatali da bukatar 'Chuchu' da ake zargi da kisan Nafi'u

Lagos
An kama iyayen da su ka yi yunkurin satar da dansu Horo: Lagos State Police Command
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa wannan ikirari ya sa hukumar asibitin ta gaggauta sanar da 'yan sanda, inda su kuma su ka kawo wa yaron dauki.

"Canada za mu tafi da kudin," Iyaye

Wasu iyaye sun sanya yaronsu a kasuwa da niyyar sayar da shi saboda abin da su ka kira wahalar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da aka yi holensu a babban ofishin 'yan sandan jihar Legas, sun ce ba a son ransu su ka dauki matakin ba.

Jaridar Sahara Reporters ta wallafa cewa a na su hankalin, gwara su sayar da shi ga inda zai samu abinci da sutura.

Legas: Ƴan sanda sun yi martani Sun kara da cewa sun yi tanadin amfani da kudin da za a sayi dansu wajen tafiya kasar Canada ko sa samu saukin rayuwa. Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa tuni su ka ceto yaron, kuma ana zurfafa bincike kan iyayen.

Kara karanta wannan

Mai rabon ganin badi: 'Yan bindiga sun saki yaran alkaliya da aka sace a Kaduna

An sace jariri a Legas

A baya mun ruwaito cewa 'yan sanda sun cafke wata mata da ake zargi da satar jariri dan wata daya a jihar Legas.

Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya ce an kama Blessing mai shekaru 21 bisa zargin lallabawa ta dauke yaron har cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.