An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da yaro a Kano

An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da yaro a Kano

Rahotanni sun nuna cewa masarautar Kano ta dakatar da mai unguwar Sabon Gari, mallam Ya'u Muhammad, bayan da aka zarge shi da hannu a wajen sayar da wani yaro mai shekara daya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da masarautar ta Kano ta fitar a daren Talata, 25 ga watan Agusta, daga ofishin Galadiman Kano kuma babban dan Majalisar sarkin na Kano, Alhaji Abbas Sanusi, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Ana dai zargin mai unguwar Malam Ya'u tare da shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar Fagge, Jamilu Yusuf da sayar da wani jariri ga wata mata kan kudi N20,000.

Mataimakin sakataren masarautar Kano, Awaisu Abbas Sanusi, ya bayyana cewa, an dakatar da mai unguwa Ya'u ne bayan rahoton da hakimin Fagge Alhaji Mamuda Ado Bayero ya gabatar a gaban sarkin Kano.

An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da jariri a Kano
An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da jariri a Kano Hoto: The Guardian
Asali: UGC

An dai dakatar da mai unguwar ne har zuwa lokacin da hukumomi za su kammala bincike.

Da farko dai mun ji cewa kwamandan hukumar Hisbah na yankin Fagge, Ustaz Jamilu Yusuf, ya shiga hannun jami'an hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP).

Hakan ya kasance ne kan zarginsa da ake da hannu a safarar wani yaro mai shekara daya.

Kwamandan rundunar NAPTIP na yankin, Shehu Umar, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da mambobin kwamitin bincike a kan hukuncin da shari'a ta dauka a kan mutanen da suka bata a Kano suka kai masa ziyara.

Ya ce, mutum biyar hukumar ta damke har da kwamandan Hisbah, wadanda ake zargi da hannunsu a ciki.

Hukumar har a halin yanzu tana bincike kafin ta dauka matakin da ya dace a kan sacewa da siyar da yaron.

Sai dai kuma hukumar ta Hisbah ta karyata rahoton cewa shugaban hukumar na Fagge ne ya sayar da yaron.

KU KARANTA KUMA: Bayan shekaru 13: Gwamna Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomin Borno

A yanzu haka dai an samu wanda suka ce suna so za su karɓi wannan yaro su ci gaba da kulawa da shi.

"Mai unguwar Sabon Gari shi ya yarda cewa za a mika wannan yaron hannun Jamila Kabir, wata mata haifaffiyar nan (Kano) aka yi yarjejeniya tsakanin kwamandanmu da mai unguwa da ita Jamila Kabir amma duk wata daya za a dawo da shi mu dunga ganin halin da yake ciki wanda da ma ita ce doka." in ji Ibn Sina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel