Kano: Kotu Ta Fusata da Ɗabi’un Ganduje, Matarsa da Wasu 6, Ta Ba da Sabon Umarni
- Mai shari'a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta yi hukuncin kan bukatar da aka gabatar na cafke Abdullahi Ganduje da wasu 7
- Lauyan masu kara, Adeola Adedipe, SAN, ya nemi kotun ta ba da umarnin cafko tsohon gwamnan ne saboda ya ki bayyana gaban kotu
- Sakamakon kin bayyana gaban kotu da wadanda ake kara suka yi, kotun ta ba da umarnin cigaba da shari'ar ko da basu halarta ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke hukunci kan bukatar lauyan gwamnatin jihar na ba da umarnin cafko Abdullahi Ganduje, mai dakinsa da wasu mutum 6.
Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta yi fatali da bukatar lauyan, inda ta ce ba za ta sa a kama tsohon gwamnan Kanon da sauran mutane 7 din ba.
Kotu ta fusata da dabi'un Ganduje
An gurfanar da Abdullahi Ganduje, matarsa Hafsat da wasu 7 gaban kotun ne kan zargin damfara da kuma karkatar da kudaden jama'a, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya kotun ta bayar da umarnin a bi wasu hanyoyi na daban wajen isar da takardun sammaci ga wadanda ake kara biyo bayan kin bayyanarsu gaban kotun.
A zamanta na jiya Alhamis, kotun ta fusata da kin bayyanarsu Ganduje gabanta, inda ta ba da umarnin cigaba da shari'arsu ko da ba su nan tunda sun ki gurfana duk da samun sammaci.
Lauya ya bukaci a kama Ganduje
Jaridar Leadership ta ruwaito, lauyan masu kara, Adeola Adedipe, SAN, ya shaidawa kotun cewa tun a 6 ga watan Yuni aka aika sakon sammaci ga wadanda ake karar.
A cewarsa:
"Ya mai shari'a, wadanda ake kara na 1, 2, 3, 4, 5, 7 da 7 sun ki bayyana gaban kotu ko kuma su tura wakili, wanda ake kara na 6 ne kawai ya yi hakan.
"Hakazalika, ina rokon kotun ta yi amfani da sashe na 278 na kundin dokar shari'ar ta'addanci (ACJL) ta jihar Kano domin ba da umarnin cafko wadanda ake karar."
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranakun 23 da 24 ga watan Oktoba domin sauraron korafin da da wadanda ake kara suka gabatar da kuma sauraron manyan tuhume-tuhume.
Gwamnatin Kano ta canja kotun shari'ar Ganduje
A wani labarin, mun ruwaito cewa kwamishinar shari’a ta Kano, Dije Abdu Aboki, ta sauya kotun da za ta saurari shari’ar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar da Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin Kano na tuhumar tsohon gwamna Ganduje, mai dakinsa Hafsat da wasu 6 da laifin Zamba da kuma karkakatar da kudin jama'a.
Asali: Legit.ng