Tinubu Ya Fadi Sabon Albashin da Zai Iya Biyan Ma’aikata, NLC Ta Dage Kan N250,000
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnati da kamfanoni a za su iya biyan sama da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi ba
- Sai dai shugaban ya roki kungiyar cewa za a iya canja mafi karancin albashin a cikin shekaru biyu ko uku maimakon bayan shekara biyar
- Rahotanni sun ce an dage taron Tinubu da shugabannin ’yan kwadago zuwa ranar 18 ga watan Yulin mako mai zuwa domin sake tattaunawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kungiyoyin kwadago da su amince da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya, jihohi da kamfanoni suka amince da shi.
Tinubu ya kuma tabbatarwa da shugaban kungiyar cewa za a iya a rika canja mafi karancin albashin duk bayan shekara biyu, uku ko hudu ba sai ya kai shekara biyar ba.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a shafinsa na X jim kadan bayan ganawar Tinubu da shugabannin 'yan kwadago a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya fadi mafi karancin albashi
A cewar Onanuga, taron da aka yi a fadar shugaban kasa ya samu halartar ministan tattalin arziki, Wale Edun, da kuma shugaban NNPC, Mele Kyari inda aka tattauna batun tattalin kasar.
Shugaba Tinubu ya jagoranci jami’an gwamnati a taron, ya kuma bukaci ma’aikata da su amince da N62,000 da aka gabatar matsayin matakin farko na warware matsalar mafi karancin albashi.
Sanarwar Onanuga ta bayyana cewa 'yan kwadagon sun dage akan biyan mafi karancin albashi na N250,000 kafin a dage taron har sai mako mai zuwa.
A cewar sanarwar, Tinubu ya ce:
"Me ya sa za mu rika waiwayar mafi karancin albashin duk bayan shekaru biyar? Me zai hana ba zai koma duk bayan shekara biyu ko uku ba? Matsalarmu a yau za ta iya zama sauki gobe."
Karanta cikakken bayanin anan kasa:
Gwamnati ta aika sako ga 'yan kwadago
Tun da fari, mun ruwaito cewa Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta roƙi ƙungiyoyin ƙwadago kan shirinsu na shiga yajin aiki.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Idris Mohammed yayin wata ta musamman ya buƙaci ƴan ƙwadagon da su haƙura da shiga yajin aikin.
Asali: Legit.ng