Albashi: Daga Karshe Shugaba Tinubu Ya Fadi Abin da Gwamnati Za Ta Biya Ma'aikata

Albashi: Daga Karshe Shugaba Tinubu Ya Fadi Abin da Gwamnati Za Ta Biya Ma'aikata

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana irin mafi ƙarancin albashin da gwamnatinsa za ta biya ga ma’aikatan Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya ce zai tura sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa wanda gwamnati za ta iya biya ba tare da takura ba ga majalisar tarayya
  • Da yake jawabi a wurin liyafar cin abincin dare na bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce zai sanar da majalisar dattawa idan ya canza shawara kan mafi ƙarancin albashin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta amince ne kawai da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan da za ta iya biya.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen liyafar cin abincin dare na bikin ranar dimokradiyya a ranar Laraba 12 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Albashi: Kungiyar NLC ta juyawa Tinubu baya, ta fadi gaskiyar halin da ake ciki

Tinubu ya magantu kan mafi karancin albashi
Tinubu zai biya ma'aikata albashin da gwamnatinsa ba za ta takura ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Tinubu zai aika da ƙudiri ga majalisa

Shugaban ƙasan ya ce zai sanar da Godswill Akpabio da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin idan ya sauya ra’ayi kan shawarar biyan N62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya/gwamnatocin jihohi da kuma ƙungiyoyin kamfanoni masu zaman kansu (OPS) ne suka amince da biyan N62,000.

Jaridar The Nation ta ce, an miƙa shawarar ga sakataren gwamnatin tarayya, George Akume yayin da ake sa ran Tinubu zai aika da abin da ya amince da shi a matsayin ƙudiri ga majalisar tarayya.

Nawa Tinubu ya ce gwamnati za ta biya?

"Shugaban majalisar dattawa, mataimakin shugaban majalisar dattawa, za ku sami sanarwa idan na canza shawara kan mafi ƙarancin albashi."
"Za mu yi, abin da Najeriya za ta iya, abin da za ku iya, abin da zan iya. Ana cewa ka tsaya daidai matsayinka, ka da ka ƙure kanka."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauki matsaya, zai miƙa sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa

- Bola Ahmed Tinubu

NLC ta musanta iƙirarin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta musanta iƙirarin shugaban ƙasa Bola Tinubu na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa.

Ƙungiyar ta dage cewa har yanzu tana kan buƙatar ta na neman a biya N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng