Shugaba Tinubu Zai Zauna Da Kungiyoyin Ƙwadago, Kila A Fadi Albashin Ma'aikata

Shugaba Tinubu Zai Zauna Da Kungiyoyin Ƙwadago, Kila A Fadi Albashin Ma'aikata

  • Kungiyoyin ƙwadago za su zauna da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a kan batun mafi karancin albashi da ya-ki-ci, ya-ki-cinye wa
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya gayyaci kungiyoyin kamar yadda shugaban kungiyar 'yan kasuwa (TUC), Festus Osifo ya bayyana
  • Ana sa ran shugaban kasar zai bayyana matsayar gwamnatin tarayya kan batun mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Yayin da kungiyoyin ƙwadago su ka dage cewa lallai sai gwamnatin tarayya ta yi ƙari mai gwaɓi kan albashin ma'aikata, shugaban kasa Bola Tinubu ya gayyace su fadar gwamnati. Shugaban kungiyar 'yan kasuwa (TUC), Festus Osifo ne ya bayyana cewa shugaban ya nemi tattaunawa da su a ranar Alhamis, 11 Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Karancin albashi: Bayan ragi sau 3 NLC, TUC sun ta kafe kan N250,000

Kwadago
Shugaban kasa zai tattauna da kungiyoyin kwadago ranar Alhamis Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa ana sa ran Bola Ahmed Tinubu zai bayyana matsayar gwamnatinsa dangane da mafi karancin albashin.

Ana sa ran cimma matsaya kan albashi

Jaridar The Cable ta tattaro cewa alamu masu karfi na nuni da cewa ana dab da cimma matsaya kan batun mafi karancin albashi a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan tattaunawa da za a yi gobe tsakanin kungiyoyin kwadago, kwamitin gwamnati kan mafi karancin albashi da shugaban Bola Tinubu.

Ita dai hadakar kungiyar kwadago ta ce bai kamata gwamnati ta biya mafi karancin albashi da ya gaza N250,000 ba.

Amma gwamnatin tarayya da na jihohi na ganin kamata ya yi kungiyoyin su duba halin da kasa ke ciki, kuma a bari kowace jiha ta biya abin da za ta iya.

Kungiyoyin ƙwadago sun fitar da matsaya

Kara karanta wannan

Wata miyar: Tsadar rayuwa ta sanya shugaban Liberia zaftarewa kansa albashi

A baya kun ji cewa hadakar kungiyoyin kwadago ta bayyana cewa ba za ta rage ko sisi daga bukatar da ta mikawa gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwa (TUC), Festus Osifo ne ya jaddada matsayarsu inda ya ce N250,000 bai yi yawa ba ganin halin da kasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.