Bayan Ganawa da Tinubu, 'Yan Kwadago Sun Bayyana Matsayarsu Kan Mafi Karancin Albashi
- Ƙungiyoyin ƙwadago ba su sauya matsaya ba kan buƙatar da suka nema na gwamnati ta biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
- Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa har yanzi suna nan kan bakansu na sai gwamnati ta biya hakan
- Joe Ajaero ya bayyana hakan ne bayan shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago sun gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Villa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana matsayarta kan mafi ƙarancin albashi bayan ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Joy Ajaero, ya bayyana cewa har yanzu suna nan kan bakansu na gwamnati ta biya N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin.
Meyasa ƴan ƙwadago suka gana da Tinubu?
Da yake magana da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan kammala taro da Shugaba Tinubu, Ajaero ya ce shugabannin ƙwadagon sun je ne domin ganawa ba tattaunawa ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban na ƙungiyar ƙwadagon ya bayyana cewa za a ci gaba da taron a sati mai zuwa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Bayan sun gana na fiye da sa'a ɗaya, shugabannin ƙwadagon sun fito daga zaman inda suka shaidawa manema labarai cewa za su tattauna da mutanensu kafin su sake dawowa fadar shugaban ƙasan.
Shugaban ƙungiyar TUC, Festus Osifo, ya bayyana cewa sun yi wa shugaban ƙasan bayani kan matsayarsu, sannan shi ma ya yi nasa jawabin.
Sai dai, bai bayyana cikakken bayani ba kan yadda zaman na su ya kasance.
An kasa cimma matsaya kan albashi
A yayin da gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu suka amince da N62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, ƴan ƙwadago sun dage sai an biya N250,000.
Shugaban ƙasa Tinubu ya bayyana cewa yana buƙatar lokaci domin kammala shawarwari da sauran masu ruwa da tsaki kafin ya miƙa ƙudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya.
NLC ta gargaɗi gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ce ba ta gamsu da buƙaar gwamnonin Najeriya ba na basu damar yanke mafi ƙarancin albashin jihohinsu da kansu.
NLC ta ce ba gwamnoni wuƙa da nama kan sabon mafi ƙarancin albashi tamkar ba kura ajiyar nama ne, kuma hakan zai kara jefa ƙasar a tsananin talauci.
Asali: Legit.ng