Karin Albashi Ya Gagara: Yan Kwadago Sun Fara Sabuwar Gwagwarmaya

Karin Albashi Ya Gagara: Yan Kwadago Sun Fara Sabuwar Gwagwarmaya

  • Kungiyar yan kwadago sun dauki damarar taya hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) yaki da rashawa
  • Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero ya ce ya kamata dukkan yan Najeriya su hada kai da EFCC kan yaki da cin hanci a Najeriya
  • Joe Ajaero ya bayyana haka ne yayin wani gangami da hukumar EFCC ta shirya kan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta daura damarar taya hukumar EFCC yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a birnin tarayya Abuja a yau Alhamis, 11 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

'Ana shan wuya,' Wani babba a APC ya cire kunya ya koka kan mulkin Tinubu

Yan kwadago
Yan kwadago za su taya EFCC yaki. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Joe Ajaero ya buƙaci EFCC ta bude kofa ga sauran al'umma su taya ta yaki da rashawa, kamar yadda NLC ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC: 'Dole a tashi a yaki rashawa'

Shugaban kungiyar kwadago ya ce akwai buƙata mai tsanani a Najeriya kan yaki da cin hanci da rashawa.

Saboda haka ne ma yace a yanzu haka za su saka dukkan karfinsu wajen goyon bayan EFCC domin samun nasara.

NLC: 'Mutane za su taya EFCC yaki'

Joe Ajaero ya bukaci hukumar EFCC ta bude kofa ga al'ummar Najeriya domin su taya ta yaki da rashawa a Najeriya.

Ya bayyana cewa mutane da dama suna son taya EFCC yaki da barayi saboda illar da satar kuɗin gwamnati ke yiwa Najeriya.

Illar cin hanci ga Najeriya

Shugaban kwadago ya ce idan rashawa ta cigaba a Najeriya ba za a samu damar gina gobe mai kyau ba.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC, sun kashe jami'in tsaro

Ya bayyana cewa yaki da rashawa ne ke hana Najeriya cigaba ta ɓangarori gina kasa da suaransu, rahoton Punch.

Karin albashi: An gaza samun matsaya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin ma'aikata a Najeriya sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashi wanda gwamnatin tarayya ta gabatar masu yau.

Gwamnatin ta ba da shawarar a ƙara mafi ƙarancin albashin daga N30,000 zuwa N62,000 a taron kwamitin da aka kafa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng