Yadda Cin Hanci Ya Sa Ake Shirin Rusa Daukan ’Yan Sanda a Najeriya

Yadda Cin Hanci Ya Sa Ake Shirin Rusa Daukan ’Yan Sanda a Najeriya

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta bukaci rusa shirin daukan sababbin yan sandan shekarar 2022/2023 da ake kokarin kammalawa
  • Cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an samu korafi daga masu ruwa da tsaki bayan an sake sunayen wadanda aka tantance
  • Rundunar ta yi karin haske kan nau'ukan almundanar da aka saka cikin shirin wanda hakan ne ya jawo neman rusa lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Rundunar yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwa kan daukan sababbin yan sanda na shekarar 2022/2023.

Sanarwar ta yi nuni da cewa sufeton yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya bukaci rusa shirin daukan yan sanda da aka yi.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Yan sanda
An nemi dakatar da daukan aikin yan sanda a Najeriya saboda badakala. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Legit ta gano lamarin ne cikin wani sako da rundunar yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan neman rusa daukar yan sanda

1. Cusa sunayen bogi

Rundunar ta bayyana cewa an samu marasa kishin kasa sun saka sunayen waɗanda ba su nemi aikin dan sanda ba kwata-kwata.

Rahoto ya nuna cewa waɗanda aka cusa sunayensu suna da yawan gaske kuma ko mataki daya ba su taka cikin matakan neman aikin ba.

2. Cusa waɗanda suka faɗi jarrabawa

Bincike ya gano cewa an cusa sunayen wanda suka fadi jarrabawar na'ura mai ƙwaƙwalwa da aka gudanar kafin daukan aikin cikin waɗanda suka yi nasara.

Haka zalika akwai zargin sanya sunayen waɗanda suka faɗi sauran nau'ukan tantancewa da aka yi amma aka ga sunayensu.

3. Sanya sunayen marasa lafiya

Rundunar ta tabbatar da cewa an saka sunayen wadanda aka tabbatar da ba su da lafiya yayin tantancewa cikin wadanda suka yi nasarar samun aikin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi aika aika a Imo, sun kashe 'yan sanda da farar hula

A karshe rundunar yan sanda ta ce an samu yawaitar cin hanci da rashawa inda aka karbi kudin wadanda ba su da ce ba aka sanya sunayensu cikin waɗanda aka zaba domin aiki.

An kama yan bindiga a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan jihar Delta sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da dama tare da wani matsafi dauke da gashin mutane.

Ana zargin yan bindigar da aka kama da yawaita ayyukan ta'addanci a yankunan Warri, Ugheli, Sapele da sauran wurare a fadin jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng