Fintiri Ya Zargi Tinubu da Zaftare Kudin Adamawa, Sun Shiga Kotu
- Gwamnatin jihar Adamawa karkashin gwamna Ahmadu Fintiri ta shigar da gwamnatin tarayya kara gaban kotu
- Lamarin ya biyo bayan zargin da gwamnatin Adamawa tayi ne na rage mata kason kudi da gwamnatin tarayya ta yi
- Jami'in yada labaran gwamantin jihar Adamawa ya bayyana abin da suke buƙata kotu ta musu bayan shigar da karar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Rahotanni na nuni da cewa an samu saɓani tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Adamawa.
Lamarin ya kai gwamna Ahmadu Fintiri ya shigar da kara babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an samu saɓanin ne bayan zargin zaftare kudi da gwamnatin tarayya ta yi ga jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fintiri: 'Dole Bola Tinubu ya bi doka'
Gwamnatin jihar Adamawa ta ce an zaftare mata kudi daga asusun karɓar kudin wata wata daga gwamnatin tarayya.
Ta kuma bayyana cewa doka ba ta ba gwamnatin tarayya damar haka ba saboda haka ta bukaci abi doka domin bi mata hakki.
Gwamna Ahmadu Fintiri ya ce dole shugaban kasa yabi dokar rarraba rabano a tsakanin jihohin Najeriya baki daya.
Abin da Adamawa ke buƙata a kotu
Gwamnatin Adamawa ta shigar da gwamnatin tarayya gaban kotu domin neman karin bayani kan lamarin, rahoton Daily Post.
Jami'in yada labaran gwamnatin jihar Adamawa ya ce suna bukatar kotun ta musu bayani kan hukuncin zaftare kudin jihar ba bisa ka'ida ba.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan kotun tarayya da ke Abuja domin ganin bayanan da za ta yi da kuma hukuncin da za ta yanke.
An kama yan daba a Adamawa
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar da kama 'yan daba da aka fi sani da 'yan shila da suka addabi sassa daban-daban na jihar a wani samame da suka kai
Kakakin rundunar yan sanda, Suleiman Nguroje ne ya tabbatarwa manema labarai da kamen, inda ya ce cikin yan shilar da aka kama akwai mata biyu.
Asali: Legit.ng