An Kama Ɓarawon da Ya Gawurta da Satar Babur Bayan Ya Yi Sata a Asibiti
- Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta sanar da cafke gawurtaccen ɓarawo da a ake zargi ya shahara da satar babur
- Ɓarawon mai suna, Kabiru Abubakar an kama shi a yayin da ya sace babur a farfajiyar asibiti a jihar Sokoto
- Kakakin yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa'i ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a yau Laraba, 10 ga watan Yuli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta sanar da cakfe wanda ake zargi da yawaita satar babur a Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa asirin ɓarawon ya tonu ne bayan an kama shi yana kokarin guduwa a lokacin da ya sace babur.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kakakin yan sanda a jihar Sokoto ne ya bayyana lamarin ga yan jarida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɓarawo ya sace babur a asibiti
Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Sokoto ta kama Kabiru Abubakar bisa zargin sace babur a asibiti.
Kabiru Abubakar ya ce babur din ne a asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto a ranar 5 ga watan Yuli.
Bayan kama ɓarawon wanda ya mallaki babur din ya zo ya karbeta, kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.
An samu karin babura wajen ɓarawo
Bayan tsananta bincike ɓarawon ya bayyana cewa shi ya sace babur a asibitin Rahamat da ke Sokoto.
Da jami'an yan sanda suka matse shi da tambayoyi. Kabiru Abubakar ya ambaci wanda yake mikawa babura idan ya sace domin su sayar.
Daga nan kuma yan sanda suka samu karin babura guda shida da ake zargin cewa Kabiru Abubakar ne ya sace a wurare daban-daban.
An kashe barawon babur a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun fusatattaun mutane sun kashe wani ɓarawo yana ƙoƙarin satar babur a masallaci a jihar Bauchi.
An ruwaito cewa barawon ya yi yunkurin satar wani babur, lokacin da wani ya hango shi ya yi masa 'ihu barawo', inda aka rufe shi da duka.
Asali: Legit.ng