Wani 'Barawon Babur ya gurfana Gaban Kuliya a Jihar Ekiti

Wani 'Barawon Babur ya gurfana Gaban Kuliya a Jihar Ekiti

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta gurfanar da wani Matashi dan shekara 22, Mathew Tosin, a gaban Kotun Majistire dake zaman ta a Birnin Ado-Ekiti na Jihar Ekiti da laifin satar wani babur kirar Bajaj Boxer.

A halin yanzu dai Kotu na zargin Mathew da laifin Satar Babur mai darajar kimanin Naira Dubu Dari Uku da Ashirin.

Sufeto Oriyomi Akinwale, jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, Mathew dai ya aika wannan laifi ne da misalin karfe 05.30 na safiyar ranar 5 ga watan Yuni a unguwar Falegan dake Birnin Ado-Ekiti.

Wani 'Barawon Babur ya gurfana Gaban Kuliya a Jihar Ekiti
Wani 'Barawon Babur ya gurfana Gaban Kuliya a Jihar Ekiti
Asali: UGC

Kamar yadda Sufeto Oriyomi ya bayyana, wannan Babur mallakin wani Mista Daniel Okaula ne wanda Mathew ya yi awon gaba da shi ba tare

Yake cewa, Mathew ya yi awon gaba da Baburi ne mai Lambar MUS 875 QC wanda mallakin wani Mista Daniel Okaule ne.

KARANTA KUMA: Cristiano Ronaldo har ya zaɓi Lambar da zai goya a Manchester United - Rahoto

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan laifi ya sabawa sashe na 390 jikin dokokin miyagun laifuka na jihar Ekita da ta gindaya a shekarar 2012.

Mista Timi Omotosho, Lauya mai kare Mathew a gaban Kotu ya roke ta da ta bayar da belin wanda ya ke yiwa wakilci, inda Alkaliya Mrs Omolola Akosile ta biya wannan bukata akan kudi N50, 000 tare daga sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel