An zargi shugaba Buhari da sanya agogon hannu na N7,181,520 (hotuna)
An gano shugaban kasa Muhammadu Buhari sanye da agogon hannu mai tsada yayinda ya kai ziyara ga sarkin jihar Katsina.
An gano shugaban kasar sanye da agogon fata na Breguet a yayinda yaje Daura a jihar Katsina.
A cikin hotunan, an gano shugaban kasar tare da sarkin Katsina mai martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman a Daura Katsina a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba.
Binciken Legit.ng ya nuna cewa agogon Breguet ya kai kimanin dala dubu ashirin wanda daidai yake da naira 7,181,520.
Koda dai, ba’a san wani rukuni na Breguest shugabna kasar ya sanya ba, anyi hasashen cewa agogon shugaban kasar ya kai kimanin dala 16,000 zuwa daga 22,000.
A halin yanzu, yanayin shugaban kasar a cikin hotunan da ya dauka a lokacin da yake Daura sun nuna yna cikin koshin lafiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng