Ana Tsaka da Tashin Hankali a Filato, an Kamo Kurar da Ta Tsere Daga Gandun Dabbobin Jos

Ana Tsaka da Tashin Hankali a Filato, an Kamo Kurar da Ta Tsere Daga Gandun Dabbobin Jos

  • Gidan namun dajin Jos da ke jihar Filato ya sanar da cewa ya yi nasarar kamo wata kura da ta tsere daga gandun dabbobin a ranar Lahadi
  • A cewar wata sanarwa da hukumar yawon bude ido ta jihar Filato ta fitar, an gano kurar a raye bayan an gudanar da bincike mai zurfi
  • Hukumar ta ce a halin yanzu an mayar da kurar a cikin kejinta, kamar yadda ita ma hukumar gidan namun dajin ta tabbatar a wata sanarwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jos, Plateau - Rahotanni sun bayyana cewa an samu nasarar kamo wata kura da ta tsere daga gandun dabbobin Jos kuma an sameta da ranta tare da mayar da ita cikin keji.

Kara karanta wannan

Kano: Mazauna Rano na cikin tashin hankali kan Abubuwan da ke faruwa a fadar sarki

Hukumar yawon bude ido ta jihar Filato karkashin shugabancin Chuwang Pwajok ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Hukumar yawon bude ta Filato ta yi magana kan kurar da ta tsere a Jos
Kurar da ta tsere daga gidan namun daji ta shiga hannu. Hoto: Murat Özgür Güvendik/Anadolu
Asali: Getty Images

Sanarwar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa, an gano inda kurar take ne bayan zurfin bincike inda daga nan aka sumar da ita tare da kama ta, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kamo kurar da ta bace a Jos

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Muna sanar da jama’a cewa, bayan tsananta bincike, an gano kurar da ta bace inda aka yi mata allurar bacci tare da kama ta. A yanzu haka tana cikin kejinta.
"Muna matukar godiya ga jama'a saboda kasancewa cikin natsuwa da kuma bamu hadin kai, wanda ya taimaka matuka wajen bincike da ceton dabbar."

An sanar da tserewar kura a Jos

Kara karanta wannan

Jami'ar Kwara ta kori dalibai 175, an zayyana manyan laifuffukan da suka aikata

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa an shiga tashin hankali a wani yanki na karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli.

Wannan ya faru ne bayan wata kura ta tsere daga gandun dabbobin da ke yankin a ranar Lahadi, 7 ga Yulin 2024, wanda ya haifar da firgici a tsakanin mazauna wurin.

Tun a ranar Lahadin ne aka baza dakarun tsaron namun daji da ma sauran jami'an tsaro wajen ganin an nemo kurar tare da kamata kafin ta yi wata barnar.

Zaki ya cinye mai bashi abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani zaki ya kashe ma’aikacin jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Olabode Olawuyi a gandun dabbobi na jami’ar da ke Ile-Ife, jihar Osun.

A cewar wata sanarwa da jami'ar ta fitar, zakin ya kai wa Olabode Olawuyi hari ne yayin da ya ke bashi abinci, aikin da ya saba yi na fiye da shekaru tara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.