Yadda yaki ke barazanar gushewar dabbobin daji a nahiyar Afrika

Yadda yaki ke barazanar gushewar dabbobin daji a nahiyar Afrika

- Namun daji na fuskantar barazanar karewa a dazukan nahiyar Afrika saboda yawaitar yake-yake

- Sojoji da 'yan ta'adda dake na cinye dabbobin dake dazukan a matsayin abinci

- Kungiyoyin kare gandun daji da hakkin dabbobi na bukatar a dauki matakan gaggawa kafin dabbobi su kare

Wasu kungiyoyin kare gandun daji da hakkin dabbobi sun ja hankalin duniya a kan barazanar da namun daji ke fuskanta a dazukan nahiyar Afrika saboda yawaitar yake-yake.

Wani bincike na wata kungiya (Conservation group) ta bayyana cewar fiye da kaso 70% na namun daji dake dazukan nahiyar Afrika daga shekaru 60 da suka wuce babu su a yanzu.

Yadda yaki ke barazanar gushewar dabbobin daji a nahiyar Afrika
Yadda yaki ke barazanar gushewar dabbobin daji a nahiyar Afrika

DUBA WANNAN: Sanatan Najeriya ya fusata, ya yi gargadi da babbar murya ga 'yan uwansa Sanatoci

Shugabar wata kungiya, Margaret Kinnairda, ta ce bayan yake-yake, sojoji na farautar hauren giwa da kahon karakanda domin su sayar su sayi makamai.

Ta yi kira ga gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika da su gaggauta raya dazuka da zarar an samu zaman lafiya a duk kasar dake fama da yaki domin bawa dabbobin damar dawowa dazukan.

A yanzu haka dangin gwagwgwon biri da wasu namun dajin daga kasashen Afrika da dama sun tare a wani surkukin dajin kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo (DR Congo).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel