Gwamna Ya Kori Shugabannin Makarantun Sakandare 7, Sun Karɓi Kuɗi Daga Ɗalibai
- Gwamnatin jihar Taraba ta ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare bakwai bisa zargin yin zagon kasa ga ilimi a jihar
- Kwamishiniyar ilimin jihar, Misis Augustina Yahaya ce ta sanar da dakatar da shugabannin makarantun bakwai a sanarwa da ta fitar
- Misis Yahaya ta ce an kori shugabannin makarantun saboda sun karbi kudi daga hannun dalibai wanda ya saba da tsarin gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jalingo, Taraba - Gwamnatin jihar Taraba ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare bakwai bisa zargin yin zagon kasa ga ilimi a jihar.
Ma'aikatar ilimi ta jihar ta ce shugabannin makarantun suna karbar kudi daga hannun dalibai wanda ke kawo cikas ga shirin Gwamna Agbu Kefas na ba da ilimi kyauta a jihar.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar, Misis Augustina Yahaya ce ta sanar da dakatar da shugabannin makarantun guda bakwai a cikin wata sanarwa da ta fitar, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Misis Augustina Yahaya ta ce dukkanin wadanda abin ya shafa sun aikata laifuffukan da nufin kawo cikas ga nasarorin da aka samu a shirin ba da ilimi kyauta da gwamnan ya bayyana.
Dalilin korarar shugabannin makarantun
Kwamishiniyar ta ce:
“An dakatar da shugaban makarantar sakandaren gwamnati ta Jauro Yino saboda karbar kudi daga hannun dalibai na NECO.
"An dakatar da shugaban makarantar Yakasali da ke Wukari saboda karbar kudi da sayar da guraben zana jarabawar WAEC ga daliban waje.
“An dakatar da shugaban makarantar GDSS Kakulu da ke Zing saboda sakaci da rashin sa ido yayin da ya hana dalibai 105 yin rijistar jarrabawar kammala karatunsu.”
Sauran shugabannin da aka dakatar
Sauran shugabannin makarantun da gwamnatin jihar ta dakatar sun hada da na shugaban makarantar GDSS Kofai da Salihu Dogo a Jalingo.
An kuma kori shugabannin makarantun GDSS Kununi da ke Lau; GDSS Jouro Yinu da ke Ardo-Kola; GDSS Kakulu da ke Zing; GSS Takum, da kuma GDSS Yakassai da ke a Wukari.
Gwamna ya rabawa makarantun sakadare N450m
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya raba Naira miliyan 450 ga makarantun sakandire 100 na jihar.
Gwamna Radda ya raba kuɗin ne a wani biki da aka gudanar a makarantar sakandaren gwamnati ta Doro a ƙaramar hukumar Bindawa inda ya ƙaddamar da kashi na biyu na shirin AGILE.
Asali: Legit.ng