Jami’ar Kwara Ta Kori Dalibai 175, an Zayyana Manyan Laifuffukan da Suka Aikata

Jami’ar Kwara Ta Kori Dalibai 175, an Zayyana Manyan Laifuffukan da Suka Aikata

  • Akalla dalibai 175 ne aka kora daga jami'ar jihar Kwara (KWASU) da ke Malete, bayan an kamasu da aikata laifuffuka daban daban a makarantar
  • Hukumar gudanarwar jami’ar ta ce laifuffukan sun hada da satar amsa, shiga haramtattun kungiyoyi, mallakar bindiga da sauran su
  • A cikin wata sanarwa da ta fitar, jami'ar KWASU ta jaddada cewa ba za ta saurarawa daliban da ke aikata laifuffukan rashin da'a ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kwara - Hukumar gudanarwar jami’ar jihar Kwara (KWASU), Malete, ta kori dalibai 175 na jami’ar bisa wasu laifuffuka daban-daban da suka aikata.

Amincewar korar ya biyo bayan shawarwarin kwamitin ladabtarwa na ɗalibai (SDC), wanda ya gudanar da zama tsakanin Oktoba 2021 da Maris 2024.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya fara samun koma baya, shugabannin NNPP sun koma APC

Jami'ar Kwara ta yi magana kan dalibai 175 da ta kora
Jami'ar Kwara ta kori dalibai 175 bayankamasu da laifuffukan daban daban. Hoto: @KwasuOfficial
Asali: Twitter

Jami'ar Kwara ta kori dalibai 175

Mukaddashin daraktar hulda da jami’ar, Dakta Saeedat Aliyu ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a daren Litinin, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce jami'ar KWASU ta kori daliban ne bisa kamasu da aikata laifuffukan da suka hada da satar jarrabawa da sata a cikin makaranta.

Sauran laifuffukan sun hada da yin amfani da sakamakon karya domin samun gurbin karatu, cin zarafi, damfara, shiga haramtattun kungiyoyi da kuma mallakar bindiga.

Jami'ar Kwara ta aika sako ga jama'a

A wani rahoton Channels TV, jami'ar Kwara ta ce:

"Muna sanar da jama'a cewa an kori dalibai 175 daga jami'ar jihar Kwara dake Malete bisa wasu laifufuffka da suka aikata bayan rahoton kwamitin ladabtarwar dalibai (SDC).
"Hukumar jami'ar jihar Kwara na sake jaddada matsayarta kan hukunta daliban da suke aikata abubuwan rashin da'a yayin da jami'ar ke kokarin yaye nagartattun dalibai."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

Mataimakin Bursar na jami'ar KWASU ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin Bursar na jami’ar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a lokacin da yake kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON 2023.

An ruwaito cewa hawan jinin Abdullahi ne ya tashi ana daf da kammala buga wasan, inda ya yanke jiki ya fadi yayin da aka garzaya da shi asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.