Shugaban Jami'ar Jihar Kwara, Farfesa Muhammad Akanbi, Ya Rasu

Shugaban Jami'ar Jihar Kwara, Farfesa Muhammad Akanbi, Ya Rasu

  • Allah ya yi wa VC na jami'ar jihar Kwara (KWASU), Farfesa Muhammad Akanbi, rasuwa ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, 2020
  • Rahotanni sun nuna cewa za'a masa Jana'iza ranar Litinin a gidansa dake Ilorin, babu bayanin abinda ya yi ajalinsa
  • Gwamna jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya miƙa sakon ta'aziyyarsa tare da Addu'ar Allah ya sa shi Aljanna

Kwara - Shugaban jami'ar jihar Kwara (KWASU), Farfesa Muhammad Akanbi, ya rigamu gidan gaskiya yana da shekara 51 a duiya.

An ce ya rasu ne ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, 2022 kuma wasu majiyoyi da muka tattara sun nuna cewa za'a yi jana'izarsa a gidansa dake Ilorin ranar Litinin.

Farfesa Muhammad Akanbi.
Shugaban Jami'ar Jihar Kwara, Farfesa Muhammad Akanbi, Ya Rasu Hoto: Bukola Saraki
Asali: Facebook

Jam'ar KWASU ce ta sanar da rasuwar shugabanta a wata sanarwa da ta saki a shafin facebook da daren ranar Lahadi.

"Ya rasu ne ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022 bayan rashin lafiya ta ɗan lokaci. Muna rokon ɗaukacin al'umma su sa iyalansa da jami'a a Addu'a a wannan lokaci na jarabawa. Za'a sanar da lokacin jana'izarsa nan gaba kaɗan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Akanbi, shi ne babbam ɗan marigayi shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC), Mai shari'a Mustapha Akanbi.

Marigayin, babban Lauya a Najeriya (SAN) ya zama shugaban jami'ar jihar Kwara da ke Malete a shekarar 2019.

Gwamnan Kwara ya yi ta'aziyya

Tun bayan samun labarin rasuwarsa, sakonnin ta'aziyya suka ci gaba da fitowa daga sassa daban-daban inda gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya jagoranci masu jimami.

A sakon ta'aziyyarsa da yammacin ranar Lahadi, Gwamna AbdulRazaq, ya bayyana rasuwar VC da abun takaici da kaɗuwa, "Amma ya zama wajibi mu rungumi kaddara domin Allah ne mai bayarwa da ɗauka."

A shafinsa na Facebook, Gwamnan ya ce:

"Muna jajanta rasuwar shugaban jami'a wanda ya koma ga mahaliccin mu da daren nan. Mutumin kirki ne kuma bawan Allah, muna rokon Allah SWT mai rahama da gafara ya sa Aljannar Firdausi ta zama makomarsa."

A wani labarin kuma duk da rigimar dake tsakanin FG da ASUU, Tsohon Ministan Buhari, Rotimi Amaechi, ya kammala karatun Jami'a

Tsohon ministan Sufuri, wanda ya yi murabus domin neman takarar shugaban ƙasa ya gama karatun Digirin ne a jami'ar Baze dake birnin tarayya Abuja.

Bayanai sun nuna cewa Amaechi na cikin ɗalibai sama da 500 da smaka yaye, ya karanci ilimin shari'a LLB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel