Yahaya Bello Ya Koma Matsala, EFCC Ta Nemi Taimakon Kasashe a Kama Tsohon Gwamna
- Hukumar EFCC ta nemi taimakon jami'an INTERPOL na kasashen Morocco, Tunisia da Aljeriya wajen kama tsohon gwamnan jihar Kogi
- An ce EFCC ta samu wasu bayanan sirri da ke nuni da cewa Yahaya Bello na iya tserewa zuwa daga daga cikin wadannan kasashen
- Hakazalika, wata majiya daga hukumar yaki da rashawar ta ce akwai yiwuwar hukumar ta kai samame gidan gwamnatin jihar Kogi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar EFCC ta sanya tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello cikin jerin sunayen wadanda INTERPOL za ta sanyawa ido a kasashe uku na Arewacin Afrika.
An ce hukumar EFCC ta yanke wannan hukunci ne bisa sahihan bayanan sirri da ta samu, inda ta nemi taimakon Morocco, Tunisia da Aljeriya wajen kama Yahaya Bello.
Hukumar EFCC ta kunnowa Yahaya Bello wuta
Sauran kasashen da EFCC ta nemi taimakon jami'an INTERPOL wajen kama Yahaya Bello sun hada da Masar, Libya da Sudan, kamar yadda rahoton jaridar Leadership ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta ce akwai bayanan sirri da ta samu da ke nuni da cewa Yahaya Bello na iya tserewa zuwa daya daga cikin wadannan kasashen.
An fitar da jerin kasashen ne gabanin ranar 17 ga watan Yuli da ake sa ran tsohon gwamnan zai gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.
Yahaya Bello na 'yar buya da EFCC
Jaridar The Nation ta ruwaito majiyoyi daga EFCC sun ce hukumar tana dab ta kai samame gidan gwamnatin jihar Kogi, inda ake kyautata zaton tsohon gwamnan ya boye a can.
Yahaya Bello na fuskantar tuhume-tuhume 19 da suka shafi safarar kudi, zagon kasa da kuma karkatara da kudin gwamnatin Kogi kusan N80.2bn.
Duk da cewa tsohon gwamnan ya musanta zargin, amma ya kasa gurfana a gaban Mai shari'a Emeka Nwite a ranakun 13 ga watan Yuni da 27 ga watan Yuni.
Gwamnatin Najeriya ta nemi taimakon INTERPOL
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta nemi agajin ‘yan sandan Duniya na INTERPOL wajen kama wasu mutum uku da ake zargin sun saci kudi daga CBN.
An ce wasu ne suka yi amfani da sa hannun Muhammadu Buhari wajen fitar da dala miliyan 6,23 daga asusun bankin CBN kamar yadda rahoton mai bincike Jim Obazee ya nuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng