"Yunwa Za Ta Kashe 'Yan Najeriya," Jigo a APC Ya Nemi Daukin Shugaba Tinubu

"Yunwa Za Ta Kashe 'Yan Najeriya," Jigo a APC Ya Nemi Daukin Shugaba Tinubu

  • Jigo a jam'iyyar APC ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan duba halin yunwa da ake ciki
  • Mista Olatunbosun Oyintoloye ya shaidawa manema labarai a Osogbo ranar Lahadi cewa mutanen Najeriya na cikin yunwa
  • Ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu ya yi watsi da rahoton majalisar dinkin duniya cewa za a yi yunwa a kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun- Jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Olatunbosun Oyintiloye ya bayyana cewa 'yan kasar nan na cikin matsananciyar yunwa. Mista Olatunbosun Oyintiloye ya bayyana haka a Osogbo, babbar birnin jihar Osun a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

An kama jagora a PDP, Atiku Abubakar ya zargi 'yan sanda da cin zarafin 'yan kasa

Bola Tinubu
Jigo a APC ya shawarci Shugaba Tinubu ya kawo karshen yunwa a Najeriya Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro jigon ya ce matsin da ake ciki ya hana 'yan kasar nan ita ɗora tukunya sau uku a rana.

"Tinubu ya dauki mataki yanzu," Oyintoloye

Jigo a jam'iyyar APC, Olatunbosun Oyintoloye ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta shawo kan matsalar yunwa a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa 'yan Najeriya na cikin matsi, yunwa da rashin samun kudin gudanar da rayuwarsu ta yau da gobe, Sahara Reporters ta wallafa.

Ya shawarci Bola Tinubu ya yi watsi da hasashen majalisar dinkin duniya na cewa 'yan Najeriya Miliyan 82 ya su fada cikin matsananciyar yunwa zuwa shekarar 2030.

"Za mu iya kawar da yunwa," Manoman Kano

Shugaban gamayyar kungiyar manoma na kasa reshen jihar Kano, Abdullahi Ali Mai Biredi ya ce manoman Najeriya za su iya hana tabbatuwar hasashen yunwa kan kasar nan.

Kara karanta wannan

Abdullahi Ganduje: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shugabancin jam'iyyar APC

Ya shaidawa Legit Hausa ta wayar tarho cewa gwamnati ce ta gaza taimaka masu da tallafi a lokutan da su ka dace.

Mai Biredi ya ce mafi yawancin 'yan Arewa sun koma gona, amma rashin bayar da tallafi daga gwamnati da matsalar tsaro a wasu sassan yankin na barazana ga noma.

"Ba a nan kawai ake yunwa ba," Tinubu

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce ba a Najeriya kawai ake fama da yunwa ba.

Ya bayyana haka ne ga tawagar 'yan majalisa da su ka kai masa ziyara lokacin sallah babba a jihar Legas, inda ya ce 'yan kasa su yi hakuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.