Tallafin N729bn: Ministar Buhari Ta Shiga Matsala, Kotu Ta Karbi Korafin SERAP
- Wata babbar kotun tarayya ta nemi tsohuwar ministar harkokin jin kai da ta bayar da ba'asin yadda ta batar da N729bn a shekarar 2021
- Ma'aikatar jin kai a lokacin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi ikirarin cewa ta rabawa talakawa 24.4m kudin a cikin watanni shida
- Sai dai kungiyar SERAP ba ta gamsu da wannan lamari ba, inda ta garzaya kotu domin a tilastawa tsohuwar ministar ta fadi gaskiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta waiwayi tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar-Farouq kan badakalar N729bn.
Babbar kotun ta nemi Sadiya Umar-Farouq da ta yi bayani dalla-dalla yadda ta kashe N729bn da ta ce ma'aikatarta ta rabawa talakawa 24.3m a watanni shida.
Kotu ta titsiye ministar Buhari
Jaridar The Punch ta ruwaito kotun ta kuma umurci tsohuwar ministar da ta bayar da jerin sunayen wadanda suka ci gajiyar kudin, jihohin da suka fito, da kudin da kowace jiha ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’a Deinde Isaac Dipeolu ne ya yanke hukuncin a watan Yuni biyo bayan wata bukata ta ‘yancin bayani mai lamba: FHC/L/CS/853/2021, wadda kungiyar SERAP ta shigar.
Kungiyar SERAP ta samu kwafin gaskiya na hukuncin kotun a ranar Juma’ar da ta gabata, kuma ta wallafa hukuncin kotun a shafinta na X.
Kalli abin da kungiyar ta ce a kasa:
N729bn: Hukuncin kotu kan bukatar SERAP
A hukuncin da ya yanke, jaridar Premium Times ta ruwaito Mai shari’a Dipeolu ya ce:
“Tanade-tanaden dokar 'yancin bayar da bayanai ga kowanne mutum ciki har da SERAP sun tilastawa tsohuwar ministar amsa bukatar da aka gabatarwa kotun.
Don haka na ba da umarni tare da tilastawa tsohuwar ministar da ta bayar da cikakkun bayanan yadda ta kashe N729bn da ta ce an rabawa talakawan Najeriya 24.3m a 2021.”
Mai shari’a Dipeolu ya umarci tsohuwar ministar da ta baiwa SERAP cikakken bayanin yadda aka zabo wadanda suka ci gajiyar kudin, jihohinsu da kuma hanyoyin biyan kudin.
EFCC ta tsare Sadiya Umar-Farouq
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) ta riƙe tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouk, inda har ta kwana a hedikwatarta da ke Abuja.
Jami'an hukumar EFCC sun tasa Sadiya da tambayoyi domin tatsar bayanai kan badaƙalar wani kwantiragin Naira biliyan 72 da aka yi a ƙarƙashinta.
Asali: Legit.ng