Babu abin gani-a-yaba duk da kudin da aka batar a tsarin SIP a 2020 inji Ndume

Babu abin gani-a-yaba duk da kudin da aka batar a tsarin SIP a 2020 inji Ndume

- Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi magana a kan tsare-tsaren SIP

- Ali Ndume ya ce ba a ganin tasirin kudin da gwamnatin tarayya ta kashe

- ‘Dan Majalisar ya yi kira ga matasa su sa ido ga inda ake kai tulin kudin

Jaridar Punch ta ce a ranar Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021, shugaban kwamitin harkar sojojin kasa a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya soki tsarin SIP.

Sanata Ali Muhammad Ndume, ya koka da cewa babu wani abin kwarai da za a gani kuma a nuna duk da makudan kudin da aka batar a kan wannan shiri a 2020.

‘Dan majalisar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a Abuja, inda ya tattauna game da yadda aka aiwatar da kasafin kudin shekarar bara.

Sanata Ali Ndume ya yi kira ga matasa da sauran wadanda aka fito da wannan tsari domin su amfana, da su sanya wa ma’aikatan gwamnatin tarayya ido sosai.

KU KARANTA: Manyan barayi su ka zagaye Buhari - Ndume

Gwamnati ta ware kudi Naira biliyan 729 wajen aikin tallafa wa marasa galihu da karamin karfi.

Ndume yace idan har matasan da aka yi niyyar yi wa dawainiyar, da kungiyoyi da ‘yan jarida ba su sa ido kan inda kudin suke tafiya ba, ba za a cinma manufar ba.

Sanatan na Borno ya yaba, amma ya ce da sake. “Maganar gaskiya, shugaban kasa Buhari ya yi na sa. Babu gwamnatin da ya yi aiki sosai irin wannan ga matasa. "

“Amma sai masu cin moriyar tsarin sun rika tambayar ina kudinsu ke.” Sanatan ya ce sabon shirin ba matasa 774, 000 aiki zai rage yawan masu zaman banza.

KU KARANTA: Ba za a taba manta wa da ni ba – Buratai ya yi sallama da gidan Soja

Babu abin gani-a-yaba duk da da kudin da aka batar a tsarin SIP a 2020 inji Ndume
Sanata Ali Ndume Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

Ndume wanda ya koka cewa ba a ganin tasirin kudin da ake batar wa, sannan ya ce akwai tallafin da za a ba matasa da talakawa a kasafin kudin shekarar 2021.

Kwanakin baya kun ji Sanata Ali Ndume ya na cewa rashin isassun kudi da sojojin Najeriya su ke fama da shi ya hana ya yi kira a sauke shugabannin hafsoshin tsaro.

Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawar ya shaidawa manema labarai cewa bai cikin masu bada shawarar a sauke shugabannin hukumomin tsaro.

A makon nan ne mai girma Muhammadu Buhari ya yi canji a gidan sojan, ya nada sababbin hafsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel