Sheikh Sani Rijiyar Lemu Ya Kawo Mafita 1 da Za Ta Zama Silar Karshen Ta’addanci a Yau

Sheikh Sani Rijiyar Lemu Ya Kawo Mafita 1 da Za Ta Zama Silar Karshen Ta’addanci a Yau

  • Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi nasiha ta musamman a kan masu rike da madafan iko a Najeriya
  • Shehin malamin ya ce dole ne a hukunta mai laifi idan ana so zaman lafiya da kwanciyar hankali ya daure
  • An saba jin mutum ya yi ta’adi har a damke shi, amma daga karshe sai a ji labarin ya cigaba da yawo a gari

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - A lokacin da laifuffuka su ka addabi al’umma, musamman Kano da Arewacin Najeriya, malamai su na ta maganganu.

A irin haka ne aka ji Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya fito ya na yin kira ga masu rike da mulki da sauran gama-gari.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya fallasa gwamnati, an gano Uba Sani yana ‘karya’ da ayyukan El-Rufai

Sani Umar Rijiyar Lemu
Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yana so a rika yin kisasi a Najeriya Hoto: @Ya_Abdoo/Getty Images
Asali: UGC

Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi nasiha

Bajimin malamin addinin musuluncin ya yi magana ne a shirin fatawa da ya saba yi cikin mako domin amsa tambayoyin jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A musulunci akwai abin da ake kira kisasi, ma’ana hukunta wanda ya aikata laifi gwargwadon nauyin wannan laifi a addini.

Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu wanda babban malami ne a jami’ar Bayero da ke Kano ya ce wajibi ne a rika yin kisasi.

Fa'idar kisasi a addinin musulunci

Idan mutum zai aikata laifi, sannan hukuma ta kyale shi ba tare da an yi masa hukunci ba, malamin ya ce ba za a zauna kalau ba.

A musulunci ana yanke hannun barawo idan ya saci dukiya mai yawa, sannan mutum zai rasa gabbansa idan ya nakasa na wani.

Nasihar ta zo ne yanzu da a musamman jihar Kano ake kuka da barayin waya da masu satar abubuwan hawa da kuma ‘yan daba.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Gwamna Bago ya umarci dukan malamin Musulunci a zaman makoki

Rijiyar Lemu ya ce hukuma na sakaci

Rijiyar Lemu ya yi zargin ana sakacin hukunta wadanda aka kama da laifin kisa ko makamantansu, hakan zai zama darasi ga wasu.

A nasiharsa ta ranar Asabar, ya ce dole hukumomi da masu fada a ji da masu fada a al’umma su tabbatar da zaman lafiya a kasa.

Masu danyen aikin suna samun kwarin guiwar yin barna idan suka ga ba a yin hukunci a maimakon hukuma ta sa kowa ya shiga taitayinsa.

Duk wani cigaba da gwamnati za ta kawo, muddin ba a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, ya ce an yi a banza ne.

Samoa: Rijiyar Lemu da malamai sun yi huduba

A baya an samu labari cewa Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya ja-kunne kan bala’in da na’am da auren jinsi zai iya jawowa.

Malaman addini sun yi hudubobi a kan mimbaran Juma’a, sun dauki zafi a kan batun yarjejeniyar Samoa da gwamnatin kasar ta shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng