Samoa: Hudubobin Malamai Sun Dura Kan Tinubu Saboda Tsoron Halatta Auren Jinsi
- A hudubobin Juma’a da aka yi, an ji yadda aka yi inkarin amincewa aure da dangantakar jinsi a Najeriya
- Malaman addinin musulunci a fadin kasar nan sun nuna ba za su yi na’am da abin da zai kare luwadi da madigo ba
- Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi magana yayin da jama’a su ka tsorata da yarjejeniyar Samoa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Malaman addinin musulunci da-dama sun fito sun yi magana bayan jin labarin Najeriya ta shiga yarjejeniyar Samoa.
Abin da ya jawo surutu da korafi shi ne ganin cewa akwai batun halatta aure da dangantakar jinsi a wannan yarjejeniya.
Labarin ya karade gari ne bayan wani rahoto da Daily Trust ta fitar a safiyar Alhamis, sai aka yi sa’a an tado batun daf da Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hudubobi sun tabo yarjejeniyar Samoa
A hudubobin da aka gabatar a garuruwa dabam-dabam, malaman addinin musulunci sun nuna ba za su goyi bayan alakar jinsi ba.
Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu wanda malami ne a jami'a a hudubarsa ta Juma’a ya yi tir da yadda aka amince da yarjejeniyar.
Shehin malamin ya ce bayan an shiga halin wayyo Allah saboda zunuban da ba su kai luwadi ba, ana neman kawo fasadi a kasa.
Malamin musulunci ya misalta lamarin da masifar da ta fi kowace tare da bayanin irin hukuncin addini a kan luwadi da madigo.
Samoa: Sheikh Gadon Kaya ya soki yarjejeniyar
Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya yana cikin wadanda suka yi magana a kan lamarin a mimbarin Juma’a, har ya soki gwamnati.
Gadon Kaya ya ce bai dace a sa hannu a yarjejeniyar ta Samoa ba da amincewar al’umma ba tun ana mulkin damaukaradiyya ne.
Malami ya yi maganar Samoa a shari'a
A shafin X, Muammar Gaddafi ya daura hudubar Barista Ishaq Adam inda aka ji yana tsokaci game da batun ta fuskar dokar kasa.
Malamin ya tunawa jama’a a kundin tsarin mulki. Najeriya ta na da dokar haramta auren jinsi da ta sha gaban yarjeniyar ta Samao.
"Addinai sun haramta auren jinsi" - Malami
Ana da labari cewa Dr. Bashir Aliyu Umar ya ce musulmai da kirista duk sun yi inkarin auren jinsi a hudubar Juma'ar da ya gagabatar.
Babban malamin ya gargadi hukuma a kan bude kofar halatta luwadi da madigo, ya na mai jan kunne cewa hakan zai kawo masifa.
Asali: Legit.ng