Samoa: Bashir Aliyu Umar ya Fadi Matakin da Majalisar Shari’a Za Ta Dauka a Kan Gwamnati

Samoa: Bashir Aliyu Umar ya Fadi Matakin da Majalisar Shari’a Za Ta Dauka a Kan Gwamnati

  • Bashir Aliyu Umar yana cikin wadanda suka yi magana game da yarjejeniyar Samoa a hudubar ranar Juma’ar nan
  • Malamin ya ce majalisarsu ta shari’ar addinin musulunci ta kafa kwamiti da zai yi nazari yarjejeniyar da aka shiga
  • Dr. Bashir Umar ya ja hankalin mahukunta tare da bayanin matsayin auren jinsi a addinin musulunci da kiristanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Dr. Bashir Aliyu Umar babban malamin musulunci ne a Najeriya, yana cikin malaman da ake jin maganarsu a kasar nan.

A hudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Al-Furqan da ke unguwar Nassarawa a Kano, ya tabo batun yarjejeniyar nan ta Samoa.

Samoa
Majalisar kolin shari’ar addinin musulunci za tayi nazarin Samoa Hoto: @FredrickNwabufo
Asali: Twitter

Samoa: Bashir Aliyu Umar ya yi magana

Kara karanta wannan

Samoa: Hudubobin malamai sun dura kan Tinubu saboda tsoron halatta auren jinsi

A wani fai-fai da wani mai suna Izala ya wallafa X, an ji Dr. Bashir Aliyu Umar yana bayanin matsayar malaman musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban malamin ya gargadi hukuma a kan bude kofar halatta luwadi da madigo, ya na mai jan kunne cewa hakan zai kawo masifa.

Hudubar malamin ta nuna musulmai ba za su yi na’am da duk abin da zai ba ‘yan luwadi da madigo da masu auren jinsi kariya ba.

Masanin hadisin ya nuna kazantar namiji ya nemi namiji ko mace ta aikata hakan, y ace musulunci da kiristanci sun haramta hakan.

Majalisar shari'a za ta duba yarjejeniyar Samoa

Bashir Aliyu Umar ya ce sun ji ministoci biyu sun yi karin haske cewa shiga yarjejeniyar Samoa ba ta nufin an yarda da auren jinsi.

Amma duk da haka, malamin ya ce majalisar kolin shari’ar addinin musulunci ta kafa kwamiti da zai duba yarjejeniya da aka shiga.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Uba Sani ya mayar da basaraken da El-Rufai ya tsige kan kujerarsa

Masana za su duba kowane layi na wannan yarjejeniya da ta jawo abin magana, sai a fahimci gaskiyar halin da aka jefa ‘yan kasa.

Malamin musuluncin yake cewa sai bayan kwamitin ya gama aikin ne sannan majalisar kolin shari’ar musulunci za ta dauki matsaya.

Bayan jan-kunne da ya yi, shehin malamin ya kara da cewa ba za su yi na’am da muradun wasu kasashen da ba su da kishin Najeriya ba.

Malaman addini sun yi hudubobi a kan Samoa

Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya ja-kunne kan bala’in da na’am da auren jinsi zai iya jawowa kamar yadda aka rahoto dazu.

Sannan Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan amincewa da Samoa ba tare da tuntubar jama’a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng