Karin Kudin Lantarki: Kungiyar NLC Ta Aika Sabuwar Bukata ga Gwamnatin Tinubu

Karin Kudin Lantarki: Kungiyar NLC Ta Aika Sabuwar Bukata ga Gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar kwadago ta koka kan karin kudin wuta da aka yiwa masu shan wuta a tsarin 'Band A' daga N206.80/KWh zuwa N209.5/KWh
  • A yayin da take neman a gaggauta janye karin kudin wutar, NLC ta zargi gwamnatin tarayya da nuna halin rashin rko in kula da rashin gaskiya
  • A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa karin kudin wutar ya nuna girman kan gwamnati

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kwadagon Najeriya ta yi kira ga gwamnati da a gaggauta janye karin kudin wutar lantarki da kamfanonin DISCOs suka yi ga abokan huldar na tsarin “Band A”.

Kara karanta wannan

Jihar Adada: Muhimman abubuwa 5 game da shirin kirkirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas

Daga ranar 1 ga Yuli, 2024, masu shan wutar lantarki a karkashin tsarin "Band A" za su biya N209.5/KWh maimakon N206.80/KWh da suke biya a baya.

NLC ta soki gwamnatin tarayya kan karin kudin wutar lantarki
NLC ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta janye karin kudin wutar da DISCOs suka yi. Hoto: NLC
Asali: Twitter

NLC ta zargi gwamnati da 'rashin gaskiya'

A cikin wata sanarwa da ya aike wa jaridar The Punch, shugaban kungiyar NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya bayyana karin a matsayin "tsantsar rashin adalci da girman kai".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwadagon ya yi gargadin cewa karin kudin wutar zai tilasta wa kamfanoni da yawa hakura da kasuwanci tare da haifar da karin matsaloli ga 'yan Najeriya.

A yayin da take neman a gaggauta janye karin kudin wutar da aka yi, kungiyar ta NLC ta kuma zargi gwamnatin tarayya da nuna halin rashin rko in kula da kuma rashin gaskiya.

NLC ta soki gwamnati kan karin kudin wuta

Jaridar Leadership ta ruwaito kungiyar MAN ta yi gargadin cewa, karin kudin wuta da aka yi a kwanan baya ya haifar da cikas ga kasa baki daya tare da rufewar kamfanoni 300.

Kara karanta wannan

Ana kukan tsadar rayuwa, kamfanin KAEDCO ya kara kudin shan wutar lantarki

Ajaero ya tuna cewa a lokacin yajin aikin 'yan kwadago na baya bayan nan, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin janye karin kudin wutar, inda ya yi mamakin yadda a yanzu aka kara yin wani karin kudin.

Ya ce sabon karin kudin da aka yi, maimakon rage kudin da aka yi alkawari, ya nuna rashin gaskiya da rashin sanin mutuncin alkawari da gwamnati ta nuna.

KAEDCO ya kara kudin wutar lantarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin Kaduna Electric (KAEDCO) ya sanar da karin kudin wuta ga abokan huldarsa da ke kan tsarin 'band A' daga N206.80/kwh zuwa N209.5/kwh.

Sanarwar ta ce wannan karin kudin ya fara aiki ne a ranar 1 ga Yuli, 2024, amma an fitar da sanarwar karin ne a ranar 3 ga Yuli, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.