Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Mayar da Basaraken da El Rufai Ya Tsige Kan Kujerarsa

Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Mayar da Basaraken da El Rufai Ya Tsige Kan Kujerarsa

  • Mai girma Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya mayar da Cif Jonathan Zamuna, sarkin Piriga kan kujerarsa
  • Tsohon Gwamna El-Rufai ne ya tuɓe basaraken daga karagarsa a shekarar da ta gabat kafin miƙa mulki ga magajinsa
  • Gwamna Uba Sani yace ya zame masa dole ya bi dokar kotu domin hakan ta yanke a kan batun tsige basaraken

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya mayar da nadin Sarkin Piriga, Cif Jonathan Zamuna, wanda tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya sauke daga kujerarsa.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa dole ne ya yi biyayya ga hukuncin da kotu ta yanke kan tsige basaraken.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi a shirye yake, zai karɓi kowacce dokar gwamnatin Sokoto

Gwamnatin Kaduna ta bi umarnin kotu kan mayar da wani basarake mulki
Kaduna: Uba Sani ya mayar da sarkin da El-Rufai ya kora. Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Gwamna ya mayar da sarki kan mulki

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, gwamnan ya sanar da mayar da basaraken a ranar Alhamis yayin wani taron majalisar sarakunan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce:

"A matsayin alamar mayar da hankali da nayi wurin bin doka, ina son in sanar da ku cewa zan bi umarnin da kotu ta bayar a ranar 10 ga Yunin 2024.
"Kotun ta bayar da umarnin a mayar da Sarkin Piriga, da ke a ƙaramar hukumar Lere, Mai martaba Jonathan Zamuna kan kujerarsa."

"Shugabanci nagari shi ne jigo" - Uba Sani

Gwamnan jihar na Kaduna ya ce shugabanci nagari ne ke zama babban jigo wajen shawo kan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Gwamnan ya yi nuni da cewa sarakuna su ne mafi kusa da jama'a kuma shugabancinsu ne wanda ke da saurin kawo gyara a tsakanin al'ummar, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

An sanya ranar da gwamna zai mika sandan girma ga sabon sarkin Ibadan

Idan za a tuna, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai ya sauke Cif Jonathan Zamuna a ranar 22 ga Mayun 2023, kwanaki kaɗan kafin mika mulki ga Uba Sani.

Sanusi II ya zama sarkin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon Sarkin Kano bayan da ta rushe masarautun jihar biyar.

Tun bayan shan rantsuwa da Abba Kabir Yusuf ya yi a watan Mayun 2023 ake ta sa ran zai dawo da tsohon sarkin Kano da Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel