Hargitsi Ya Tashi a Majalisar Wakilai, Ana Zargin Mataimakin Kakaki da Nuna Bambanci

Hargitsi Ya Tashi a Majalisar Wakilai, Ana Zargin Mataimakin Kakaki da Nuna Bambanci

  • Wani lamarin mai kama da rikici ya ɓarke tsakanin mataimakin kakakin majalisar wakilai da wani ɗan majalisa, Cyril Hart
  • Hon. Cyril Hart ya zargi Ben Kanu da ware duk sababbin zuwa majalisar a duk lokacin da ake muhawara muddin shi yake shugabanta
  • Kalu ya musanta hakan amma Hart ya fusata tare da neman a ba su dama, lamarin da ya kai ga ya fice daga zaman majalisar kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - A ranar talata ne ɗan majalisar wakilai, Cyril Hart ya zargi mataimakin kakakin majalisar, Ben Kalu, da ware sabbin zuwa majalisar yayin tattaunawa a zauren.

Hon. Cyril, wanda zuwansa na farko kenan a majalisar daga mazaɓar Bonny/Degema a jihar Ribas, ya yi wannan zargin ne yayin muhawarar harin bam a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi a shirye yake, zai karɓi kowacce dokar gwamnatin Sokoto

Dan majalisar wakilai ya tayar da kura a zauren majalisa
Dan majalisar wakilai ya zargi kakakin majalisar da nuna bambanci. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisar wakilai ta tattauna kan harin Borno

Ɗan majalisa Ahmad Jaha daga jam'iyyar APC ne ya miƙa buƙatar tattaunawar kan ƙunar baƙin waken, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin muhawarar, Kalu ya ba da dama ga tsohon mataimakin kakakin majalisa, Idris Wase, shugaban kwamitin sojin ruwa, Yusuf Gagdi, da shugaban kwamitin tsaro, Babajimi Benson, da su bada gudumawarsu.

Duk da mambobi masu yawa sun nuna son yin magana kan lamarin, Hon. Kalu yace ba zai bari a cigaba da tattauna maganar ba saboda babu lokaci.

Majalisa: Ana zargin Kalu da nuna bambanci

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin da mataimakin kakakin majalisar yake ƙoƙarin bada damar yin ƙuri'a kan batun, Hon. Hart ya dakatar da hakan a fusace.

Hon. Hart ya zargi mataimakin kakakin majalisar da ware sababbin mambobi, inda ya ce manyan 'yan majalisar kaɗai ya bai wa damar magana kan lamarin.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta binciki tashin bam a Borno, ta dora laifin kan jama'ar yankin

Ya yi iƙirarin cewa, ya zama ɗabi'ar Kalu a koda yaushe yayin da yake shugabantar zama ya bada fifiko ga manyan 'yan majalisar.

"Ba ka ba da fifiko ga 'yan zuwan farko... ba ka bayarwa. Hakan kake yi kodayaushe. Akwai buƙatar ka baiwa sababbin zuwa damar yin magana."

- Hon. Cyril Hart

Hon. Cyril ya fice daga zaman majalisa

Sai dai mataimakin kakakin majalisar bai yi gum da bakinsa kan wannan zargi ba, inda ya kare kansa da cewa:

"Babu banbanci a wannan majalisar."

Cike da rashin gamsuwa da kalaman Hon. Kalu, dan majalisar na Ribas ya cigaba da jawabi duk da kashe makirfo ɗinsa da aka yi, daga bisani kuma ya fice daga zauren majalisar.

Majalisa ta dauki mataki kan harin Borno

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa ɗan majalisa mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar wakilai, ya ce sakacin jama'a da jami'an tsaro ne ya jawo harin bam a Borno.

Kara karanta wannan

Ana cikin matsalar abinci, Sarkin Katsina ya shiga sahu, ya jagoranci sallar roƙon ruwa

A yayin da ya gabatar da kudurin gaggawa kan harin kunar bakin waken da aka kai yankin Gwoza, dan majalisar ya nemi da a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.