'Yan Bindiga Sun Harbe Malamin Jami’ar Katsina Har Lahira, Sun Sace Ƴaƴansa
- Wasu 'yan bindiga sun kai sabon farmaki a rukunin gidajen Yarima Quarters, da ke a karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina
- A yayin farmakin, an ruwaito cewa 'yan bindigar sun kashe wani malamin jami'ar tarayya ta Dutsinma, Dakta Tiri Gyan David
- Shugaban jami'ar FUDMA, Farfesa Armaya'u Bichi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce 'yan bindigar sun sace mutane hudu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Dutsinma, Katsina - Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malami a jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina.
An ruwaito cewa an kashe Dakta Tiri Gyan David a wani sabon harin da ‘yan bindiga suka kai a safiyar ranar Talata.
'Yan bindiga sun kashe malamin FUDMA
Wani ganau ya shaida wa Channels TV cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na dare a gidan malamin da ke unguwar Yarima Quarters, a karamar hukumar Dutsinma, jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Dakta Tiri Gyan David ya kasance mataimakin shugaban sashen jami'ar na koyar da tattalin arzikin noma, da raya karkara
An kuma ruwaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin dauke da miyagun makamai, inda suka rika harbe-harbe ta ko ina domin tsorata mazauna yankin.
'Yan bindigar sun tafi da mutane hudu
Shugaban jami'ar FUDMA, Farfesa Armaya'u Bichi ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Guardian.
Farfesa Armaya'u Bichi ya ce:
"Sun kashe daya daga cikin malamanmu, Dakta Tiri Gyan David, mataimakin shugaban sashen koyar da noma. Sun kashe shi kuma sun tafi da 'ya'yansa guda biyu."
"Sun kuma shiga gidan wani Mista Adeola, sun yi awon gaba da kannensa guda biyu amma ba a tafi da wasu ma'aikatan jami'ar biyu da ke gidansa a lokacin ba."
Abuja: 'Yan bindiga sun sace yara 2
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari kauyen kauyen Guto da ke Bwari, birnin tarayya Abuja, inda suka sace kananan yara mata guda biyu.
Sai dai an ce jami'an tsaron hadin guiwa da suka hada da 'yan sanda, DSS da mafarauta sun samu nasarar yiwa 'yan bindigar kwanton bauna tare da kwato yaran.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng