Tsohon Sanata Ya Fadi Kuskuren Buhari da Ya Kamata Tinubu Ya Kiyaye

Tsohon Sanata Ya Fadi Kuskuren Buhari da Ya Kamata Tinubu Ya Kiyaye

  • Sanata Shehu Sani ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya riƙa duba cancanta wajen naɗa muƙamai a gwamnatinsa
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya gargaɗi Shugaba Tinubu kan yin irin kuskuren magabacinsa, Muhammadu Buhari
  • Ya nuna cewa idan shugaban ƙasan yana son ya samu sakamako mai kyau, sai ya mayar da hankali wajen duba cancanta kafin naɗa muƙamai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ba da fifiko wajen duba cancanta yayin naɗa muƙamai.

Shehu Sani ya gargadi shugaban ƙasan da kada ya yi irin kuskuren magabacinsa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tsohon jigon APC ya wanke Tinubu kan halin da Arewa ke ciki, ya fadi mai laifi

Shehu Sani ya ba Tinubu shawara
Shehu Sani ya ba Tinubu shawara kan nada mukamai Hoto: Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunday Politics' a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba Tinubu?

Shehu Sani ya ce a lokacin gwamnatin Buhari na shekara takwas tsakanin 2015 zuwa 2023, an nuna son zuciya wajen naɗa muƙamai amma duk da haka ba a samar da sakamako mai kyau ba.

"Zan shawarci shugaban ƙasa Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan kada ya tafka kura-kurai na shugaba Buhari, kuma na yi imanin cewa yana da ƙwarewar da zai fahimci hakan."
"A ƙarƙashin Shugaba Buhari, akwai ministoci da aka naɗa a kan muƙamansu tsawon shekaru takwas, sun kasance tare da shi a zangon farko da na biyu, kuma babu wani garambawul na majalisar ministoci."
"Ko da an cire wani, sai an ɗauki watanni uku zuwa huɗu kafin a maye gurbin minista. Haka aka gudanar da mulkin ƙasar."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno, ya fadi matakin dauka

"A ƙarƙashin Buhari mun ga ƙololuwar son zuciya inda aka naɗa mutane muƙamai kuma aka barsu ko da ba su yi komai ba."

- Sanata Shehu Sani

Ya bayyana cewa idan Tinubu yana son samun sakamako mai kyau, cancanta ya kamata ta zama abin da zai fi bayar da muhimmanci a kai.

Shehu Sani ya ba shugabanni shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga shugabannin Arewa da su ba ilmi muhimmancin gaske.

Sanata Shehu Sani ya buƙace su da su ɗauki ilimi da gaske domin kaucewa rugujewar makarantun gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel