Tsohon Sanata Ya Bayyana Bangaren da Tinubu Ya Yiwa Buhari Fintinkau

Tsohon Sanata Ya Bayyana Bangaren da Tinubu Ya Yiwa Buhari Fintinkau

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kwatanta matsalar rashin a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu
  • Shehu Sani ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a lokacin gwamnatin Buhari ta fi muni fiye da lokacin gwamnatin Bola Tinubu
  • Ya bayyana cewa za a iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro idan gwamnati ta nuna da gaske take yi kan shawo kan matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan ƙalubalen rashin tsaron da Arewacin Najeriya yake fuskanta a lokacin Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Tsohon sanatan ya yi iƙirarin cewa ƙalubalen tsaron da Arewacin Najeriya ya fuskanta a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fi na Shugaba Bola Tinubu muni.

Kara karanta wannan

NLC: Bola Tinubu ya samu saƙon mafita kan mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Shehu Sani ya yi magana kan rashin tsaro
Shehu Sani ya ce an fi samun tsaro a lokacin Tinubu fiye da Buhari Hoto: Shehu Sani, Buhari Sallau
Asali: UGC

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin cika shekara 40 na ƙungiyar tsofaffin ɗaliban kwalejin kimiyyar gwamnati da ke Kagara a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya gudana ne a makarantar sakandire ta Ahmadu Bahago da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Shehu Sani, ya ce taron na da nufin baiwa tsofaffin ɗaliban damar tuna baya da yin tunani kan yadda za a sake buɗe makarantar.

Me Shehu Sani ya ce kan rashin tsaro?

Ya bayyana cewa za a magance matsalolin tsaro kwata-kwata idan gwamnati ta nuna da gaske take yi.

"Matsalolin rashin tsaro za su zo ƙarshe a ƙasar nan saboda abin da yake a yanzu yafi wanda yake a lokacin gwamnatin Buhari."
"Akwai hujja cewa da yawa daga cikin manyan ƴan ta'adda jami'an tsaronmu su hallaka su. Sannan idan aka kwatanta halin da ake ciki a yanzu, ya fi wanda ake ciki a baya. Na yanzu ya fi na baya."

Kara karanta wannan

Ana cikin matsalar rashin tsaro, Shettima ya fadi shirin Tinubu kan 'yan bindiga

"A lokacin gwamnatin Buhari, an sha kai hare-hare a makarantu da suka haɗa da jami'ar Green Field a Kaduna, Bathel Batist school a Kaduna, makarantar kimiyyar gwamnatin tarayya a Kagara."
"Makarantar sakandiren mata ta Yauri, makarantar aikin noma a Mando, makarantar sakandiren kwana ta Kankara, makarantar sakandiren Jangebe, dukkansu a gwamnatin Buhari. Saboda haka muna fata abubuwa za su gyaru."

- Shehu Sani

Yadda Shehu Sani ya ceci Obasanjo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda suka yi fama a gidan yari tare da tsohon shugaban ƙasa cif Olusegun Obasanjo.

Shehu Sani ya fadi yadda waɗanda aka haɗa su a ɗaki suka yi yunƙurin yiwa tsohon shugaban ƙasan na Najeriya duka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng