2027: Shehu Sani Ya Bayyana Matakin da 'Yan Siyasar Arewa Suka Dauka Domin Kayar da Tinubu

2027: Shehu Sani Ya Bayyana Matakin da 'Yan Siyasar Arewa Suka Dauka Domin Kayar da Tinubu

  • A makon da ya wuce manyan yan siyasar Arewa sun yi tururuwa zuwa Daura wajen tsohon shugaban kasa da Muhammadu Buhari
  • Cikin manyan yan siyasa da suka je wajensa akwai babban dan jam'iyyar adawa, Atiku Abubakar da jigo a APC, Nasir Ahmed El-Rufai
  • Legit ta tattauna da Sharif Baba Lawal kan ko zai yarda da maganar Shehu Sani ya marawa Tinubu baya a zaben shekarar 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Al'umma na mayar martani kan ziyarar da yan siyasar Arewa ke kaiwa ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura.

Sanata Shehu Sani ya ce hakan na nuna wata maƙarƙashiya da ake shiryawa Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Suna neman kassara Tinubu", Kungiyar Arewa ta caccaki Atiku da El Rufai kan ziyartar Buhari

Shehu Sani da Tinubu
Shehu Sani ya caccaki yan Arewa kan yunkurin kayar da Bola Tinubu. Shehu Sani|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zuwan 'yan siyasa wajen Buhari

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa duk da yan siyasar Arewa na fakewa da gaisuwar Sallah amma ba haka bane dalilin zuwansu wajensa.

Shehu Sani ya ce suna kulla yadda za su yi taron dangi ne ga shugaba Bola Tinubu domin dawo da mulki Arewacin Najeriya a 2027.

Illar dawo da mulki Arewa a 2027

Sanatan ya ce yan siyasar ba su duba irin hadarin da dawo da mulki Arewacin Najeriya zai iya haifarwa a kasar.

Ya ce dawo da mulki Arewa zai haifar da hadari mai girma ga hadin kan Najeriya kasancewar dan Kudu wa'adi daya ya yi a kan mulki bayan saukar Buhari.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ƙasurgumin ɓarawo a Bauchi, ya sace N120m da kayayyaki rututu

2027: Abin da talakawa za su yi

Shehu Sani ya ce ya kamata talakawan Arewa su juya baya ga yunkurin kayar da Bola Tinubu a shekarar 2027.

Ya ce hakan ya zama dole ganin yadda yan Arewa suka kasa tabuka komai a shekaru takwas da Muhammadu Buhari ya yi.

Legit ta tattauna da Sharif Baba Lawan

Wani dan Arewacin Najeriya, Sharif Baba Lawal ya ce maganar da Shehu Sani ya yi kan kin juyawa Tinubu baya a 2027 tana kan hanya.

Sharif ya ce lallai babu dalilin da zai hana shi zaben Tinubu a 2027 musamman ma idan shugabannin Arewa suka ce a juya masa baya.

Atiku ya kai ziyara jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a inuwar PDP ya kai ziyarar barka da Sallah ga Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar a Minna, jihar Neja.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana haka a shafinsa ranar Laraba, 19 ga watan Yuni kwanaki kaɗan bayan hawan idin Babbar Sallah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng