Ina Aka Kai Maƙudan Kuɗin da Aka Ƙwato Daga Ɓarayin Ƙasa a Mulkin Buhari?

Ina Aka Kai Maƙudan Kuɗin da Aka Ƙwato Daga Ɓarayin Ƙasa a Mulkin Buhari?

  • Tsohon shugaban kwamitin bincike na musamman kan kwato kadarorin gwamnati, Okoi Obono-Obla, ya yi magana kan yaki da rashawa
  • Obono-Obla yi yi ikirarin cewa an mayar da dukiyar da kwamitin sa ya kwato a lokacin tsohon gwamnatin Buhari ga barayin kasar
  • Ya kuma yi ikirarin cewa wasu jami'an gwamnatin Buhari ne suka rika yin zagon kasa ga dukkanin shirin gurfanar da barayin da ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani tsohon shugaban kwamitin kwararru da aka kafa domin bincike da kwato kudin jama'a da aka sace, Okoi Obono-Obla ya fadi inda aka kai kudaden.

Mista Obono-Obla ya yi ikirarin cewa dukkanin kudin da aka kwato a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari an mayar da su ga barayin kasar ne.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni 20 da suka ƙi yarda a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihohinsu

Okoi Obono-Obla ya yi magana kan kudin da aka kwato daga barayin kasa
Okoi Obono-Obla ya fallasa inda aka kai kudin sata da aka kwato a zamanin Buhari. Hoto: Okoi Obono-obla, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta gaza a wajen yaki da cin hanci da rashawa, gwamnatin da ya ce al'ummar Najeriya suka dorawa yarda in ji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obono-Obla, wanda Buhari ya nada shi matsayin hadiminsa, ya yi wannan ikirarin ne a ranar Asabar a yayin tattauna da wata kafar labarai, Mic On Podcast.

Nakasu a gurfanar da barayin kasa

SPIP dai kwamitin bincike ne mai zaman kansa da Buhari ya kafa domin kwato kudi da kadarorin kasar da aka sace.

A cewar Obono-Obla, kokarin da ya yi na ganin an gurfanar da masu wawure dukiyar kasa a gaban kotu, ya samu nakasu daga wasu jami’an gwamnatin Buhari.

Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, wanda shi (Obono-Obla) ya bayyana a matsayin ‘mai mulki’ na daga cikin wadanda suka kawo tsaikon.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin kwamishinonin Legas da Tinubu ya ba manyan mukamai a gwamnatinsa

Badakalar shigo da motocin sulke 80

Obono-Obla ya ce:

“Wasu daga cikin abubuwan da na kwato an mayar da su ga barayin. Misali, akwai wani lokacin da na kwato sababbin motocin X-class Mercedes Benz (masu sulke) sama da 80 a Jabi, Abuja hannu wani mutumi.
"Na tuntubi hukumar kwastam da hukumar shige da fice kan ko suna da masaniyar shigo da motocin, suka ce 'a'a', amma Malami ya hana ni daukar mataki akai, wai bai aike ni ba."

Badakalar sanata mai boye kudi a waje

Obono-Obla ya ci gaba da cewa:

“Akwai kuma batun wani sanata wanda a lokacin yana kan kujerar sa kuma daga baya ya zama shugaban majalisar dattawa, shi ma na ci karo da badakalar da ya tafka.
"Na sami bayanan a cikin takardun Panama, wanda ya bayyana cewa yana da dukiya a kasashen waje, Ba ni da hurumin bincikensa saboda kudin na kasar waje.
"A lokacin na nemi taimakon shugaban hukumar NIA, wanda ya tabbatar mun da zargina, amma Malami ya hana ni daukar mataki akai, har yanzu ba a kara tado da maganar ba."

Kara karanta wannan

Sabon mafi ƙarancin albashi: Gwamnoni 17 sun aikawa Tinubu muhimmiyar buƙata

Kalli tattaunawar a nan kasa:

Kudin da aka kwato daga 2015 zuwa 2022

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta sanar da cewa ta kwato dala biliyan 1 na kudaden da mahandama suka wawure a kasar nan daga 2015 zuwa 2022.

Abubakar Malami, Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a na kasar (na wancan lokacin) ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.