Gwamnatin tarayya ta sake kwato Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati
Kwamitin nan na musamman da Shugaba Buhari ya kafa domin kwato kadarorin gwamnati dake a hannun ma'aikatan gwamnati ya ce ya samu nasarar kwato akalla Naira biliyan 4, dala miliyan 7 daga hannun barayin gwamnati.
Shugaban kwamitin da aka dorawa alhakin kwato kadarorin, Mista Okoi Obono-Obla shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishin sa a garin Abuja.
KU KARANTA: Daliban jami'ar ABU sun ciri tuta a fannin fasaha
Legit.ng Hausa ta samu kuma cewar sa, kimanin dalar Amurka miliyan 7 ce aka samu a cikin wani asusun ajiya na bankin Heritage da wani tsohon jami'in gwamnati ya boye wadanda kuma kudin na haram ne.
A wani labarin kuma, Shari'ar da Sanata Dino Melaye, Sanatan dake wakiltar mazabar jihar Kogi ta gabas dake a gaban alkalin wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Abuja, babban birnin tarayya a unguwar Maitama ta gamu da sabuwar tangarda.
Mun samu cewa alkalin kotun dai ya katse zaman sauraron shari'ar ne a dai dai lokacin da daya daga cikin shaidun masu kara yake bayar da sheda akan tuhumar da ake yi wa Sanatan saboda rashin bin doka wajen gabatar da shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng