Abubakar Malami SAN ya na dawo da yakin da ake yi da barayi baya - Lauya
- Oluwatosin Ojaomo ya ce Ministan shari’a ya na kawo cikas wajen yaki da rashin gaskiya
- Lauyan ya ce ofishin AGF ya na hana a binciki wasu da ake zargi da laifin satar dukiyar kasa
- Itse Sagay ya yi na’am da wannan zargi, ya ce AGF ya kan tadiye kafar gwamnatin Buhari
Oluwatosin Ojaomo, lauyan gwamnati da ya yi aiki da kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin karbo dukiyoyin sata ya zargi minista da maida agogon gwamnatin tarayya baya.
Mista Oluwatosin Ojaomo ya bayyana cewa ministan shari’a Abubakar Malami (SAN) ya ki bada damar a nemi kotu ta karbe wasu daruruwan kadarorin sata da aka bankado a kasar.
Lauyan ya ke cewa kwamitin SPIP sun yi bincikensu tun 2019, kuma sun mikawa ministan shari’a takardu kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni.
A Satumban 2019 ne shugaban kasa ya ruguza wannan kwamiti, ya kuma bukaci ofishin AGF ya karbe duk wasu ayyukan da SPIP ya yi wanda jaridar Punch ta ce sun haura 500.
A cewar Lauyan, Abubakar Malami ya ki gurfanar da wadannan takardu a gaban kotu, wanda hakan ya sabawa umarnin shugaban kasa da kuma dokar laifuffuka na 2015.
Lauyan ya bada misali da lamarin Ibrahim da Tijjani Tumsah, wanda ya ce an dawo masu da gidaje da motocinsu har 86 bayan kwamitinsu ya yi nasarar karbe su daga hannunsu a da.
KU KARANTA: Laifuffukan da ake zargin Magu da aikatawa a hukumar EFCC
Ibrahim tsohon darekta ne a ma’aikatar gwamnatin tarayya, yayin da ‘danuwansa Tijjani kuma ya rike shugaba a ma’aikatar PINE kuma ya na cikin shugabannin rikon kwaryar APC.
Ojaomo ya ce an maidawa wadannan ‘yan gida daya kadarorinsu bayan kwamitin Okoi Obono-Obla ya karbe dukiyoyin na su, kuma ministan shari’a ya ki yin abin da ya kamata.
Jami’in gwamnatin ya ce wannan mataki da ministan shari’a ya dauka ya nakasa yaki da rashin gaskiya da wannan gwamnati ta ke yi domin ana barin barayi su na watayawa.
“Na rubutawa minista takarda ya bani damar cigaba da aiki, ana maganar bincike 600 ne.” Mista Ojaomo ya ke cewa Malami ya hana sa cigaba da aikinsa a matsayinsa na Lauya.
Da aka tuntubi hadimin ministan, Umar Gwandu, ya karyata wadannan zargi, ya ce ba gaskiya ba ne, a cewarsa ma a dalilin Malami ne gwamnatin Buhari ta ke samun nasarori.
Farfesa Itse Sagay wanda ke ba shugaban kasa shawara wajen yaki da sata ya nuna bai yi mamakin jin wannan labari ba, ya ce ofishin AGF ya na hana ayi wasu binciken da su ka kamata.
Ba wannan ba ne karon farko da ake zargin Abubakar Malami da zama alakakai wajen yakin da gwamnatin APC mai-ci ta ke yi wajen yaki da rashin gaskiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng