Gwamnatin Tarayya zata kwato $7b daga bankuna, kudade da aka basu bashi tun 2008
- Dole bankuna su dawo da kudin da gwamnati ta ranta musu
- Ba kyauta aka basu ba, mallakin yan Najeriya ne
- Zamu karbo, tare da hukunta duk wanda muka samu da laifin killace dukiyar da ba tashi ba
Kwamitin shugaban kasa ta musamman, akan dawo da kudin al'umma zata karbo dala biliyan 7 da aka ara wa bankuna masu zaman kansu a tsakanin 2006 da 2008.
Shugaban kwamitin, Okoi Obono-Obla ya sanar da hakan a ranar juma'a a garin Abuja.
Mista Obono-Obla yace ba kyauta aka ba bankunan ba kuma dole su dawo da su.
"A yanzu haka muna bincike da yawa akan kudaden da aka kwashe."
"Daya daga ciki shine dala biliyan 7 da babban bankin Najeriya ya ara wa bankuna masu zaman kansu a 2006,2007 da 2008.
Bayan shekarun nan basu dawo dashi ba, da muka tambaya babban bankin Najeriya, sai suka ce ai kyauta aka basu."
"Kudin mallakin yan Najeriya ne, don haka baza'a ba bankuna masu zaman kansu ba, wanda wasu mutane suka mallake su."
Yace kungiyar ta shirya tsaf don karbo kudaden, tare da dawo ma da Gwamnatin tarayya su.
Mista Obono-Obla yace akwai wani katon fili, mallakin wata cibiya a karkashin ma'aikatar noma da raya karkara. Wasu yan Najeriya marasa kishin kasa suka siyar dashi.
DUBA WANNAN: Doyin Okupe ya dawo aiki
"Ina tabbatar muku shima zamu kwato shi, sannan mu hukunta masu hannu a ciki."
"Akwai wasu kadarorin NPA dake Calabar, Warri, Koko, Sapele da Legas. Suma zamu karbo su." inji Obono-Obla
Ya hori yan Najeriya dasu taimaka da duk wasu labarai da suka San zasu taimakawa kungiyar don kwato kadarorin Gwamnatin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng