Sanata Ya yiwa Tinubu da Talakawa Hannunka Mai Sanda Ganin Abin da Ya Faru a Kenya
- Shehu Sani yana ganin cewa abin da ya faru kwanan nan a kasar Kenya ya nuna irin karfin da talaka yake da shi
- Tsohon ‘dan majalisar ya kamanta zanga-zangar da aka yi a kasar Afrikan da irin na End SARS da ya karade Najeriya
- Sanata Shehu Sani ya na tsoron ranar da irin haka za ta faru a kasar nan, wasu fusatattun matasa sun aukawa majalisa
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ganin abubuwan da suke faruwa a kasar Kenya, Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa a shafin sada zumunta na zamani.
Fitaccen ‘dan siyasar kuma tsohon ‘dan gwagwarmya ya yi magana ganin yadda al’ummar Kenya suka taso gwammatinsu a gaba.
A dandalin X, Sanata Shehu Sani ya kamanta matsin lambar da shugaba William Ruto ya sha a Kenya da gwagwamayar EndSARS.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya ce abin da ya faru izina ce ga shugabannin da ke rike da kasashen Afrika.
Idan za a tuna, mutane sun huro wuta a shekarar 2020, da karfi da yaji aka wargaza dakarun EndSARS da ake zargi da cin zarafi.
Irin haka ta faru kwanan nan a kasar Kenya, mutane su ka barke da zanga-zanga domin nuna adawa da wani kudirin tattalin arziki.
Sakon da Sanatan yake nunawa shi ne talakawa su da ikon bankara gwamnatinsu.
Kenya: Abin da Sanata Shehu Sani ya rubuta
"Zanga-zangar End SARS ya jawo aka ruguza sashen ‘yan sandan da ke muzgunawa jama’a."
"Sannan zanga-zangar Kenya ta tursasawa gwamnatin Ruto janye kudirin da ya jawo rikici."
"Wannan shi ne karfin al’umma."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya tsokani Sanatoci kan waki'ar Kenya
A can kuma Sanatan ya yi barkwancin da ya saba, yake tsokanar wasu abokan aikinsa a lokacin da ya wakilci Kaduna a majalisa.
Talakawan kasar Kenya sun shiga har majalisar tarayya, su ka yi ta’adi, Shehu Sani yana tunanin a ce irin haka ta faru a birnin Abuja.
Kwamred ya ce ya san Bukola Saraki garau yake, amma da wahala irinsu Ahmad Lawan da Godswil Akpabio su iya gudu da kyau.
A can yake cewa idan matsala ta taso, Dino Melaye zai iya tsere ya hau bishiya, amma Ben Murray Bruce tafiyar rangwada kurum ya iya.
An yi ram da Nnamdi Kanu daga Kenya
A can baya ana da labarin lauyoyin Nnamdi Kanu sun bukaci gwamnatin tarayya ta sake shi bayan shafe lokaci yana tsare a Najeriya.
Masu kare shi sun gabatar da hujjoji tara ga gwamnati kan shugaban na IPOB wanda tun shekarar 2021 aka kama shi a kasar Kenya.
Asali: Legit.ng