Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani

Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani

- Tsohon sanata, Shehu Sani, ya zayyano wasu abubuwa har 10 da duk wani dan Najeriya zai shiryawa kafin ya shiga siyasa

- Sanata Shehu Sani ya sha kaye a babban zaɓen da ya gabata na shekarar 2019 baya hamayyarsa da gwamna El-Rufa'i ta tilasta shi barin APC

- A cewar tsohon Sanatan, jerin abubuwa 10 shawara ce ga duk wani mutum da ya neme ya ba shi kafin ya tsunduma siyasa

Ga su kamar haka:

1. Kashewa shugabannin jam'iyya kuɗi domin samun tikitin takara duk da cewa babu tabbacin za su zaɓe ka. Amsa kira, halartar kowanne taron jama'a, sakarwa yan jagaliya mara da hakuri da wautarsu.

2. Takura, rashin samun lokacin kanka da na iyalanka sakamakon taro da jama'a koyaushe, ƙoƙarin haɗuwa da mutane da boyewa wasu mutanen.

3. Dole ka koyi kawar da kai daga zagi daga mutanen da kake ganin kafi ko sun fika ta kafafen watsa labaran na radiyo, tv da sauransu.

4. Abokan hamayyarka za su bi diddigin rayuwarka ta baya da tarihin iyayenka don samo abin suka, idan babu su kirkiro wanda za su gayawa jama'a ba. Idan ke mace ce ki shiryawa zagi kala-kala daga mazan da kika sani da waɗanda ma ba ki taɓa saninsu ba.

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

5. Idan namiji ne kai to addininka da asalin kakanninka duk sai an bibiya. Har makarantun da ka yi za su bi don jin mummunan halinka, in suka samu tarihin rashin lafiyarka ko mutuwar auren ka, za su yaɗata ga jama'a.

Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani
Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani
Asali: UGC

6. Ka shiryawa masu yaudara da son taɗe ka daga mutanen da kake son su, kila ma ka goyi bayansu ko ka taimakesu a wani abu.

7. Ka shiryawa shiga cin bashi don gudanar da yaƙin neman zaɓe, uwa uba sayar da kadarorinka da hannun jarinka wanda ka tara tsawon lokaci a rayuwarka, duk din ka tabbatar kana da kuɗi don tafiyar ta yi kyau.

KARANTA: Harin Jakana ya fusata Zulum, ya yi wa rundunar soji wata tambaya mai muhimmanci

8. Ka zama cikin shirin jin mutumin da ya ce zai taimake ka da rana ka hango shi a taron abokan hamayyarka da dare suna mitin. Ka shirya kamar ka yarda da abinda ya fada koda karya yake

9. Ka dai shiryawa shiga damuwa da tursasawa ƙwaƙwalwaka, zuciya da gangar jikinka fiye da ka'ida. Ka zauna cikin shirin jin labarai na yi maka zagon-ƙasa, barazana da rayuwarka da ta iyalanka.

10. Ka shirya bin hanya mai tsaurin gaske.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar su ashirin da uku.

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel