Mutumin da Ya yi Aiki da El Rufai Ya Yi Maganar Wawurar N423bn a Tsohuwar Gwamnati
- Ja’afar Sani ya sake yin martani ga ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna da su ka binciki gwamnatin Nasir El-Rufai
- Tsohon kwamishinan ya wanke mai gidansa, yake karyata duk zargin da ake yiwa gwamnatinsu na satar kudi jama'a
- Malam Ja’afar Sani ya ce majalisar Kaduna ta yiwa El-Rufai sharri, ta na cewa ya karbo aron wasu kudi daga ketare
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Ja’afar Sani ya yi aiki a gwamnatin Nasir El-Rufai, wanda ya karyata zargin da ake yi na cewa an karkatar da kudi.
Tsohon kwamishinan ya musanya zargin da majalisar dokokin Kaduna ta yi na cewa an sace N420bn a lokacin Nasir El-Rufai.
Majalisa ta gayyaci duka jami'an gwamnatin El-Rufai?
Imran U. Wakili wanda masoyin Malam Nasir El-Rufai ya fito da wannan zance a shafinsa na X a tsakiyar makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ja’afar Sani ya rike kwamishinanan kananan hukumomi da na masarautu da na muhalli har da ilmi a lokacin El-Rufai yana mulki.
'Dan siyasar ya ce da farko abin ya ba su mamaki domin su na jira a ji daga gare su, kawai sai aka ji labari majalisa ta fitar da rahoto.
Wani korafi da ya yi shi ne har yanzu majalisar Kaduna ta gagara ba su ainihin takardun binciken, sai da aka ji zance yana yawo a iska.
An yi karya kan bashin gwamnatin El-Rufai?
A cewarsa, an yi karya wajen fitar da bayanin bashin da gwamnatin El-Rufai ta karba, aka hada da wasu kudin da ba a karbo ba.
Idan Malam El-Rufai bai yi nasarar karbo wasu bashin da ya yi niyya ba, Ja’afar Sani ya ce babu dalilin a tambayi inda aka kai kudin.
Tsohon kwamishinan ya ce akwai alamar tambaya kan binciken da kwamitin majalisar dokoki ta yi a kan tsohuwar gwamnatinsu.
A maganarsa, an ji shi ya na cewa gwamnatin da ta shude a jihar Kaduna ta jagoranci al’umma da gaskiya ba tare da boye-boye ba.
Binciken gwamnatin El-Rufai ko siyasa?
Tsohon kwamishinan ya kara da nuna cewa abubuwan da suke faruwa da mai gidansu watau Malam El-Rufai, makircin ‘yan siyasa ne.
Amma na hannun daman nasa bai iya kama sunayen wadanda su ke zargin cewa su ne su ke neman ganin bayan tsohon gwamnan ba.
Gidan Nasir El-Rufai daya ko kuwa?
Kwanaki rahoto ya rika yawo cewa an bankado wani gidan Naira miliyan 295 da ake zargin El-Rufai ya mallaka a Dubai da ke kasar UAE.
An bayyana sunan El-Rufai a jerin wasu manyan 'yan siyasar Najeriya da jami'an tsaro da suka mallaki kadarori masu tsada a kasar wajen.
Asali: Legit.ng