‘Yar Kunar Bakin Wake Ta Dasa Bam a Borno, Mutane Sun Mutu a Wajen Biki
- Ana zargin wata mace ta yi shigar burtu, ta hallaka mutane ta hanyar tashin bam a lokacin da ake biki a jihar Borno
- Wasu mutane da suka zo halartar daurin aure a karamar hukumar Gwoza sun rasu a sanadiyyar danyen aikin
- Ba mu da cikakken bayanin rayukan da aka rasa, amma an kai harin ne yayin da ake taron aure a safiyar yau Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Borno - Labarin da yake zuwa mana shi ne an kai wani harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar rasa rayuka.
Wannan hari ya zama silar ajalin mutane da dama da suka zo halartar daurin aure a garin Gwoza da ke jihar Borno.
An tashi bam a jihar Borno
Tashar yada labaran Channels ta kawo wannan mummunan labari a yammacin Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tsoron cewa wadanda suka zo halartar wannan daurin aure suna cikin wadanda su ka rasu a sanadiyyar harin.
Baya ga haka, akwai mutane da-dama da ake tsoron cewa sun samu rauni a sakamakon wannan danyen aiki da aka yi.
Ba wannan ne karon farko da aka kai irin wannan hari a jihar Borno ba, sai dai lamarin ya lafa a ‘yan shekarun nan.
Daily Trust da ta kawo rahoton ta bayyana cewa babu cikakken bayani game da adadin wadanda aka rasa dazu.
Yadda wata mace ta tada bam a Borno
Sai dai majiya ta bayyana cewa an kai harin ne da kimanin karfe 10:00 na safiyar yau.
Wani mutumi da ya tsira ya shaida cewa wanda ta dasa bam din mace ce wanda aka gani dauke da jajiri a kan bayan ta.
Lamarin ya faru ne a yankin Tashan Mararaba da ke kusa da wani ofishin hukumar kasha gobara da yake garin Gwoza.
Rahotanni sun nuna wadanda suka samu rauni sun a babban asibitin gwamnati na Gwoza inda malaman lafiya ke duba su.
Zuwa yanzu jami’an tsaro ba su ce komai game da wannan hari ba. Haka zalika ana sauraron gwamnatin jihar Borno.
Shehu Sani ya ce tsaro ya inganta
Dazu aka rahoto tsohon sanatan Kaduna ya na cewa abubuwa sun fi taɓarɓarewa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.
Shehu Sani ya bayyana dalilansa na cewa an fi samun tsaro a lokacin mulkin Shugaba Bola Tinubu a kan magabacin nasa.
Asali: Legit.ng