Gwamnatin Borno za ta gina gidaje 1,100 a garin Gwoza
-Gwamna Babagana Zulum yayi alkawarin gina gidaje 1,100 a kauyuka guda biyu dake garin Gwoza
-Zulum ya fadi wannan maganar ne a lokacin da ya kai wata ziyara garin na Gwoza
Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta gina gidaje 1,100 a wasu kauyuka guda biyu da mayakan Boko Haram suka dai-daita a cikin karamar hukumar Gwoza. Kauyukan kuwa su ne Ngoshe da Warabe.
Gwamna Babagana Zulum ne ya furta wannan maganar a lokacin da ya kai wata ziyara garin Limankara da kuma Gwoza.
KU KARANTA:Gwamnatin Buhari ko gandun barayi, inji jam’iyyar PDP
Gwamnan a lokacin ziyararsa ya karbi shawarwari daga shuwagabannin garuruean biyu domin fada masa hakikanin wurin da za a gina gidaje 550 a ko wane kauye guda.
Gwamna Zulum ya jinjinawa rundunar sojin Najeriya bisa namijin kokarin da tayi na sake gina gadar dake hada garin Limankara da Gwoza.
Ya kuma bada umarni ga ma’aikatar ayyuka ta jihar da ta shiga cikin aikin da sojojin ke yi domin a samu kammala shi cikin sauri.
Haka zalika, Gwamnan ya ziyarci fadar Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Idrissa Timta. Sarkin ya yabawa gwamnan saboda irin ayyukan cigaban da yake gudanarwa a jihar Borno.
Zulum ya umarci hukumar daukar malamai ta jihar Borno da ta tura da malamai zuwa makarantar sakandaren gwamnati ta Gwoza wato GSS. Gwoza domin soma karatu kai tsaye.
A wani labarin kuwa zaku ji cewa, jam’iyyar PDP tayi kaca-kaca da gwamnatin Shugaba Buhari inda ta ce babu komi cikinta in banda tarin barayi.
Mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya fadi wannan maganar a cikin wani zancen da ya fitar ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba, 2019.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng