An Ba Alkalai Cin Hanci a Shari'ar Zaben Shugaban Kasa Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

An Ba Alkalai Cin Hanci a Shari'ar Zaben Shugaban Kasa Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu maganganu sun bayyana a shafukan yanar gizo cewa mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta ce Shugaba Bola Tinubu ya "gaza"
  • Wanda ya yi rubutun ya yi iƙirarin cewa an ba wa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cin hanci da rashawa
  • Wani dandali na binciken gaskiya ya binciki iƙirarin tare da bayyana sakamakonsa a wani rahoto da aka buga ranar Juma'a, 28 ga watan Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani rubutu da aka wallafa a Facebook ya danganta wata magana mai cike da cece-kuce ga mai shari'a Monica Bolna'an Dongban-Mensem, shugabar kotun ɗaukaka ƙara.

Rubutun dai ya yi iƙirarin cewa mai sharia Monica ta ce an ba da cin hanci ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Tinubu ya yi nasara a karar zaben shugaban kasa na 2023
Tinubu, Atiku da Peter Obi ne manyan 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

An yi iƙirarin ba da cin hanci kan ƙarar zaɓen 2023

A watan Satumba na 2023, kotun zaɓen shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙarar da jiga-jigan ƴan adawa suka shigar kan nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen watan Fabrairun 2023 mai cike da taƙaddama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubutun wanda aka yi a shafin Igbo Times Magazine na Facebook na cewa:

"Yanzu: Na jagoranci ƙarar zaɓen shugaban ƙasa mafi muni a tarihin Najeriya. Kuɗaɗen da aka yi mana tayi, babu wani alƙali da zai iya tsallakewa, Tinubu ya gaza sosai - Mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta nuna nadamarta."

Menene gaskiya kan batun ba da cin hancin?

Amma shin da gaske ne shugabar kotun ɗaukaka ƙarar ta ce an ba kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cin hanci? Wani dandali binciken gaskiya na Africa Check, ya yi bincike a kan hakan.

Kara karanta wannan

An bayyana lakanin Peter Obi na lashe zaben shugaban kasa a 2027

Biyo bayan binciken da ya yi, dandalin binciken gaskiyan ya yanke hukuncin cewa babu wata hujja cewa mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta yi wannan furucin da ake danganta ta da shi.

Batun takarar Peter Obi a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Ayo Olorunfemi, ya yi magana kan batun takarar Peter Obi a zaɓen 2027.

Ayo Olorunfemi ya bayyana cewa jam'iyyar ita ce ta fi dacewa Peter Obi ya yi takara a cikinta domin lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng