Kano: Masallata Sun Rasa Ransu Bayan Tirela Ta Bi Kansu Ana Tsaka da Jam'in Juma'a
- An shiga wani irin yanayi bayan wasu masallata sun rasa ransu suna tsaka da sallah a masallacin Juma'a bayan tirela ta hau kansu
- Lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024
- Hukumar kiyaye hadura ta kasa, FRSC ita ta tabbatar da haka inda ta ce akalla mutane 14 sun mutu sanadin hatsarin motar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Hukumar kiyaye haduara ta kasa, FRSC ta tabbatar da mutuwar masallata akalla 14 a jihar Kano.
Hukumar ta tabbatar da cewa masallatan sun rasa ransu bayan tirela ta kutsa cikin jam'i a masallacin Juma'a.
A ina iftila'in ya faru a Kano?
Lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura kan hanyar Kano zuwa Kaduna da misalin karfe 1:30 na rana, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FRSC ta tabbatar da cewa direban ya gagara shawo kan motar inda ya kutsa kan jama'a a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024.
Kakakin rundunar reshen jihar Kano, Abdullahi Labaran ya ce an binne tara daga cikin wadanda suka rasu a yau Juma'a da rana, Punch ta tattaro.
Kano: Ana ci gaba da basu kulawa
Labaran ya ce sauran wadanda suka samu raunuka kuma suna ci gaba da karbar kulawa a asibiti.
Ya kara da cewa yanzu haka direban ya gudu ba a san ina yake ba inda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu.
An samu karin mamata a harin masallaci
Kun ji cewa an samu ƙarin mutanen da suka rasu sakamakon harin da wani matashi ya kai Masallaci a Larabar Abasawa, karamar hukumar Gezawa a Kano.
Shafi’u Abubakar, ɗan kimanin shekaru 38 ne ya bankawa Masallacin wuta yayin da mutane ke tsaka da Sallar Asubah a watan Mayun da ya gabata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa adadin waɗanda suka rasu sakamakon kona masallata a masallacin da wani matashi ya yi sun ƙaru zuwa 23
Asali: Legit.ng