Najeriya Ta Samu Kwangila Daga Saudiya, Za a Riƙa Fitar da Nama da Waken Soya
- Najeriya da Saudiya sun shiga yarjejeniyar cinikayya, inda ake sa ran za a rika kaiwa kasar Labarabawan nama da waken suya a shekara
- Gwamnatin tarayya ta ce wannan yarjejeniyar na daga cikin kokarin Shugaba Bola Tinubu na nemowa Najeriya hanyar kudin shiga daga waje
- Tuni dai gwamnati da 'yan kasuwar da abin ya shafa suka samar da tsari na gudanar da wannan cinikayya, in ji ministan noman Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Najeriya da kasar Saudiya sun kulla wata yarjejeniyar ta fitar da tan 200,000 na jan nama da tan miliyan daya na waken soya zuwa kasar larabawar a kowacce shekara.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa wannan alakar na daga cikin yarjejeniyoyin cinikayya da aka kulla tsakanin Najeriya da Saudiya.
Najeriya ta shiga yarjejeniya da Saudiya
Sanata Kyari ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai a taron majalisar tattalin arziki na 142 a Abuja inji rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan noman ya ce tuni gwamnatin tarayya da wasu 'yan kasuwa daga Najeriya da ke cikin yarjejeniyar fitar da kayayyakin suka samar da hanyar gudanar da kasuwancin.
Kyari ya kuma shaidawa manema labarai cewa gwamnatin tarayya ta amince da wasu shirye-shirye na bunƙasa harkar noma da gwamnatin tarayya ta amince da su.
Najeriya za ta rika kai wa Saudiya kayayyaki
Jaridar TRT ta ruwaito Sanata Kyari ya ce:
"Bayan ziyarar aiki da Shugaba Tinubu ya kai kasar Saudiya a watan Nuwambar 2023, ministan noman Saudiya ya zo Najeriya a watan Mayun nan, domin tattauna batun kasuwanci.
"Jim kadan bayan komawarsa, Saudiya ta aiko mana da bukatar mu rika kai masu tan 200,000 na jan nama da tan miliyan daya na waken soya a kowacce shekara."
Dawowar shugaba Tinubu daga kasar Saudiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan ziyarar da ya kai ƙasashen Netherlands da Saudiya.
Mai girma Tinubu ya dawo ne bayan ya shafe makonni biyu baya cikin ƙasar, kuma mako ɗaya bayan an yi masa gani na ƙarshe a Saudiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng