Tinubu Ya Amince da Ba Gidaje Miliyan 3 Tallafin N50,000, an Fayyace Tsarin Shirin
- Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kawo sauki ga iyalai miliyan uku a kasar
- Tinubu ya amince da ba da N50,000 ga iyalai a duka shiyyoyin kasar har na tsawon watanni uku domin rage musu radadi
- Legit Hausa ta tattauna da wasu masu sana'o'i kan wannan tallafi da za a bayar ga ƴan ƙasa a duka yankuna shida na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da raba N50,000 ga iyalan Najeriya har miliyan 3.6.
Tallafin zai zo ne karkashin hukumar tallafawa iyalai domin rage musu radadin halin da ake ciki yanzu a kasar.
Tinubu zai tallafawa Iyalai N50,000-N100,000
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin zai kunshi akalla iyalai 50,000 zuwa 100,000 daga duka jihohin Najeriya har na tsawon watanni uku.
Yadda tsarin tallafin Tinubu zai kasance
"Shugaba Tinubu ya amince da raba tallafi ga iyalai a duka shiyyoyi guda shida da ke Najeriya karkashin hukumar tallafawa iyalai."
"Daga cikin abubuwan da ke karkashin shirin akwai siyan motoci masu amfani da gas da bas bas domin inganta al'umma."
"Za a ba da tallafin 50,000 ga iyalai akalla 100,000 a kowace jiha da ke Najeriya har na tsawon watanni uku."
Ajuri Ngelale
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da kuma hauhawan farashin kaya.
Legit Hausa ta tattauna da wasu masu sana'o'i kan wannan tallafi da za a bayar ga ƴan ƙasa.
Aishatu Abubakar da ke jaura ta yi fatali da tsarin inda ta ce a ina su talakawa za su ga tallafin.
Ta ce babban matsalar shi ne an sha yin irin wannan tallafi amma wadanda ya kamata ba su suke samu ba.
Khamis Ibrahim ya yi fatan Allah ya sa suna da rabo a tallafin da ake kokarin bayarwa.
"Ni har yau ban taba samun wani tallafi daga gwamanti ba, amma ina addu'ar Allah yasa ina da rabo a wannan karo."
- Khamis Ibrahim
Tinubu zai ba da tallafin N50,000
A wani labarin mai kama da wannan, mun kawo muku cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabuwar sanarwa kan ba 'yan Najeriya tallafin N50,000.
Wannan tallafi na daga cikin tsarin shugaban kasa Tinubu na ba da tallafin rage radadi (PCGS) domin kawowa jama'a saukin rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng