Manyan Abubuwa Sun Taso a Najeriya, Majalisa Ta Yanke Hutu Domin Tattaunasu

Manyan Abubuwa Sun Taso a Najeriya, Majalisa Ta Yanke Hutu Domin Tattaunasu

  • Majalisar dattawan ta yanke hutun babbar sallah da ta dauka domin yin zaman gaggawa kan wasu abubuwan da suka ɓullo
  • Kakakin majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a yammacin ranar Laraba
  • Har ila yau, Yemi Adaramodu ya bayyana manyan abubuwan da majalisar za ta tattauna a kai da zarar sun fara zaman yau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yanke hutun babbar sallah babu shiri domin zaman gaggawa.

Ana sa ran majalisar za ta tattauna kan mayan batutuwa ne da suka shafi cigaban Najeriya a zaman da za ta yi.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta dauki mataki bayan Tinubu ya yi biris da maganar ƙarin albashi

Majalisa
Majalisa ta yanke hutu domin zama na musamman. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe 'yan majalisa za su fara zama?

Kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ya tabbatar da cewa a yau Alhamis, 27 ga watan Yuni majalisar za ta dawo zama, rahoton Daily Nigerian.

Dama dai sai ranar Talata mai zuwa, 2 ga watan Yuli majalisar za ta kammala hutun babbar Sallah da ta ɗauka.

Me yasa majalisar dattawa ta rage hutu?

Yemi Adaramodu ya bayyana cewa akwai manyan abubuwan da suka taso da suka shafi canza tsarin mulkin kasa da majalisa za ta zauna a kai.

Ya kuma kara da cewa akwai lamuran da suka shafi zabe da wasu kudurorin da ya kamata majalisar ta zauna a kansu cikin gaggawa.

Majalisa za ta iya taƙaita hutu?

Har ila yau, Yemi Adaramodu ya bayyana cewa rage hutun bai saɓa dokar kasa ba saboda majalisar tana da damar yin hakan.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun mamaye fitaccen gari a Zamfara, dan majalisa ya nemi dauki

Ya kuma kara da cewa sun yi hakan ne domin samun damar kammala muhimman ayyukan kafin tafiya babban hutu da suka saba duk shekara.

Majalisa za ta yi doka kan gwamnoni

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da tababa kan mafi karancin albashi, Majalisar tarayya za ta samar da doka mai tsauri kan lamarin.

Majalisar ta tabbatar da shirinta na samar da dokar da za ta tilasta gwamnoni 36 a Najeriya biyan mafi karancin albashi da zarar an cimma matsaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel