Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Emefiele, an Gano Miliyoyin Daloli da Aka Wawushe
- A jiya Talata, babbar kotun tarayya da ke Legas ta yanke hukunci kan wasu makudan kudi da aka zargi Godwin Emefiele da wawushewa
- Hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta gurfanar da Godwin Emefiele a gaban kotun bisa zargin badakala
- Hukuncin da kotun ta dauka na zuwa ne bayan ta kwace wasu kadarori masu tsada da aka samu Emefiele da yin sama da fadi da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Hukumar EFCC ta yi nasara kan karar da ta shigar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
A jiya Talata ne babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta yi umurni da mayar da makudan kudi ga gwamnatin tarayya da Godwin Emefiele ya karkatar.
Jaridar Punch ta tabbatar da cewa alkalin kotun, mai shari'a C.J Aneke ne ya zartar da hukuncin bayan samun Emefiele da laifi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin da aka kwato wajen Emefiele
Mai shari'a C.J Anike ya tabbatar da mayarwa gwamnatin tarayya kudi kimanin Dala miliyan 1.4, rahoton Leadership.
Kotun ta ba da umurnin ne bayan tabbatar da cewa tsohon gwamnan babban bankin bai mallaki kudin ta hanyar kwarai ba.
Yadda shari'ar Emefiele ta faro
Tun a ranar 29 ga watan Mayu ne hukumar EFCC ta samu nasara kan kwace kudin da tsohon gwamnan ya wawushe.
Amma sai dai alkalin kotun ya ce kafin ya zartar da hukuncin sai an tabbatar da ba wanda ya fito ya nuna kudin nasa ne.
Biyo bayan rashin samun wanda ya yi ikirarin mallakar kudin duk da an baza labarin a jaridu sai kotun ta zartar da hukunci a jiya.
Bayanin lauyan hukumar EFCC
A zaman kotun na jiya lauyan hukumar EFCC, Bilkisu Buhari-Bala ta tabbatar da cewa ba wanda ya nuna kudin nasa ne tun bayan baza labarin a jaridu.
Saboda haka Bilkisu ta bayyana cewa Godwin Emefiele ya tara kudin ne ta wasu hanyoyin da suka saɓa ƙa'idar aiki da dokar kasa.
Yadda aka sace kudi a CBN
A wani rahoton, kun ji cewa wasu takardu da aka gabatarwa babbar kotun birnin tarayya Abuja sun nuna yadda mutane hudu suka kasafta $6.2m na sata.
Tawagar da shugaban kasa ya kafa domin ta binciki Godwin Emefiele ce ta gano yadda aka sace kudin daga bankin CBN da yadda aka raba su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng