Kotu Ta Taso Tsohon Gwamnan CBN a Gaba, Ta Ƙwace Wasu Manyan Kadarori a Abuja

Kotu Ta Taso Tsohon Gwamnan CBN a Gaba, Ta Ƙwace Wasu Manyan Kadarori a Abuja

  • Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu manyan gidaje da kadarorin makudan kuɗi daga hannun tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ya umarci gwamnatin tarayya ta karɓe kadarorin waɗanda galibi suke cikin birnin Abuja
  • Wannan na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan CBN ke ci gaba da fuskantar shari'a kan zargin almundahana kala daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a Legas ta bayar da umarnin kwace gidaje da wasu kadarori da suka kai N12.1bn da ke da alaƙa da Mista Godwin Emefiele.

Kotun ta kwace waɗannan kadarorin na makudan kuɗaɗe daga hannun tsohon gwamnan babban banki CBN, ta miƙawa gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

Godwin Emefiele.
Kotu ta amince da buƙatar kwace kadarorin Emefiele da duka haura N11bn Hoto: Mr Godwin Emefiele
Asali: Facebook

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ne ya bada umarnin kwace kadarorin na dindindin bayan sauraron ƙorafi daga hukumar EFCC ta hannun lauyanta, Chineye Okezie.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels tv ta ruwaito cewa a ranar 5 ga watan Yuni, Alƙalin ya amince da buƙatar lauyan hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) na kwace kadarorin na wucin gadi.

Meyasa kotu ta kwace kadarorin Emefiele?

Lauyan hukumar EFCC Oyedepo ya shaidawa kotun cewa ana zargin Emefiele ya yi amfani da wakilai ya sayi waɗannan kadarorin da kuɗin haram.

Ya bayyana sunayen ma'aikatan CBN guda biyu da wani mutum ɗaya da ya yi ritaya, waɗanda ake zargin sun haɗa baki da Emefiele wajen sayen kadarorin.

Galibin waɗannan manyan gidaje da shaguna suna kewayen babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kotu ta amince da buƙatar EFCC

Yayin da aka dawo zaman shari'ar jiya Jumu'a, 21 ga watan Yuni, 2023 babu wanda ya zo ya ƙalubalanci umarnin kwace kadarorin na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Edo: Jam'iyyar PDP ta gamu da babbar matsala ana shirin zaɓen gwamna

Daga nan kuma Chineye Okezie ta ƙara mika bukatar kwace su na har abada ga alkali.

Bayan karanta bayanan mai gudanar da bincike na EFCC, Alkalo Aneke ya amince da buƙatar kwace kadarorin na dindindin.

Kotu ta kori karar tsige shugaban EFCC

A wani rahoton na daban Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da korafin neman sallamar shugaban EFCC, Ola Olukoyede daga mukaminsa.

Wani lauya mai suna Victor Opatola shi ya ke kalubalantar nada Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa EFCC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262