Gwamnati Ta Takawa Dangote Burki, Ta Ƙaryata Zargin Shigo da Gurbataccen Man Fetur

Gwamnati Ta Takawa Dangote Burki, Ta Ƙaryata Zargin Shigo da Gurbataccen Man Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da fetur ta NMDPRA ta yi martani kan ikirarin cewa ana shigo da gurbataccen fetur Najeriya
  • A yayin da hukumar NMDPRA ta gana da dillalan mai, gwamnati ta ce zargin da matatar man kamfanin Dangote take yi ba shi da wani tushe
  • Matatar man Dangote ya zargi hukumar da ba wasu 'yan kasuwa lasisi, wadanda ke shigo da gurbataccen mai saboda ya fi arha a kasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce babu wani gurbataccen mai da ake shigo da shi Najeriya, yayin da take martani ga wani jami'in matatar man Dangote.

Gwamnatin ta yi wannan maganar ne a ranar Talata a wajen taron ganawarta da dillalan man fetur a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta haramta amfani da wasu nau'in robobi

Gwamnati ta yiwa Dangote martani
Zargin shigo da gurbataccen fetur: Gwamnati ta yiwa Dangote martani. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa taron ya mayar da hankali kan kudin man da aka tace, kalubalen hamayya da kuma matsalar shigo da kayayyakin da ake sarrafa su a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, a wajen taron, dillalan man fetur din sun shaida cewa za su rika sayen mai daga wasu wuraren duk da cewa ana sarrafa man a matatun cikin kasar.

"Ba a shigo da gurbataccen fetur" - NMDPRA

Da take magana ta hannun hukumar NMDPRA, gwamnatin ta ce tun a watan Fabrairu aka daina shigo da fetur mai dauke da sinadarin sulphur mai yawa.

Daraktan sashen DSSRI, na hukumar NMDPRA, Ogbugo Ukoha ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala ganawa da dillalan man, ciki har da jami'an matatar Dangote.

Ogbugo Ukoha ya ce:

"Babu wani gurbataccen man fetur da ake shigo da shi Najeriya. Wannan wata magana ce ta shaci faɗi da ake yaɗawa."

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Fetur: Jami'in Dangote ya zargi gwamnati

A ranar Litinin, mataimakin shugaban sashen mai da gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya zargi NMDPRA da ba wasu 'yan kasuwa lasisi suna shigo da gurbataccen mai.

Channels TV ta rahoto Mista Devakumar yana mai zargin kamfanonin mai na waje (IOCs) da bin dukkanin hanyoyi na ganin mai ya yi tsada a cikin gida domin a rika shigo da shi daga waje.

Jami'in matatar Dangoten ya ce 'yan kasuwa sun fi kaunar su sayi gurbataccen fetur da aka shigo da shi daga waje saboda yana da arha maimakon wanda aka gyara a cikin gida.

Matatar Dangote ta karya farashin dizal

A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar man Dangote ta sauke farashin da take sayar da man dizal daga N1200 zuwa N1000 a kan kowace lita ɗaya.

Bayanin rage farashin na kunshe a cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilun 2024.

Kara karanta wannan

Fetur ya yi tsada: Dillalai sun tsunduma yajin aiki, an rufe gidajen mai 2,000

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.